Gwamna Masari Na Katsina Ya Dage Dokar Hana Hawa Babur Da Dare Albarkacin Watan Maulidi

Gwamna Masari Na Katsina Ya Dage Dokar Hana Hawa Babur Da Dare Albarkacin Watan Maulidi

  • Gwamna Masari Na Katsina Ya Soke Dokar Hana Hawa Babur Da Dare Albarkacin Watan Maulidi
  • Gwamnan ya ce dokar za ta dawo aiki idan watan Maulidi ya kare nan da zuwa makon kusa da karshe na Nuwamba
  • Matsalar rashin tsaro a jihar ta Arewa ta tilastawa gwamnatin jihar haramta hawa babur da dare

Gwamnatin jihar Katsina ta soke dokar hana babura da dare a fadin jihar Katsina da ta kafa don dakile matsalar tsaro.

Hadimin Yada Labarai na Gwamna Aminu Bello Masari, Malam Al-Amin Isa ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar A Katsina, rahoton NAN.

Ya bayyana cewa Gwamna ya soke dokar ne saboda bukatuwan mutane wajen halartan tarukan Maulidi a watan Rabi'ul Awwal da aka shiga.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 2 za su ba 'yan banga AK-47, rundunar soji ta yi martani mai zafi

Akala
Gwamna Masari Na Katsina Ya Dage Dokar Hana Hawa Babur Da Dare Albarkacin Watan Maulidi

Yace mutane su cigaba da harkokinsu da dare daga yanzu zuwa karshen watan Rabi'ul Awwal Da Rabi'u Sani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Albarkacin Watan maulidi, Gwamna Masari ya amince da soke dokar hana hawa babur da dare."
"Dokan Zai dawo aiki ranar 20 ga watan Nuwamba. Saboda haka ana kira ga al'ummar gari su kasance masu biyayya ga doka."

Zaku tuna cewa irin haka gwamnatin jihar ta dage dokar lokacin watan Ramadana.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel