Babu wanda ya tsira: Har Gidan Gwamnati Na Fuskantar Barazanar Ambaliya inji Gwamna

Babu wanda ya tsira: Har Gidan Gwamnati Na Fuskantar Barazanar Ambaliya inji Gwamna

  • Gwamna Douye Diri yace Bayelsa ta shiga mawuyacin hali a sanadiyyar ambaliyar ruwan sama
  • Mai girma gwamnan ya kira taron majalisar tsaro domin a duba yadda za a bullowa lamarin a Jihar
  • Douye Diri ya yi bayanin yadda tituna suka gutsure, yayi kira ga gwamnatin tarayya ta sa dokar ta-baci

Bayelsa - Mai girma Gwamna Douye Diri yace gidan gwamnatin jihar Bayelsa yana fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a halin da ake ciki.

Jaridar nan ta Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba 2022 da ya bayyana cewa ambaliya na yi wa jihar babban barazana.

Gwamna Douye Diri ya yi wannan bayani ne yayin da ya kira wani taron gaggawa na majalisar tsaro a gidan gwamnati a babban birnin Yenagoa.

Da yake jawabi a ranar Lahadi, Mai girma gwamnan yace ya kira zama da jami’an tsaro ne domin duba halin da ake ciki da nufin a samu mafita.

Gwamnatin Bayelsa tana neman hanyar da za ta magance wannan masifa ko akalla a rage radadin da al'ummar wasu garuruwa suka shiga ciki.

Kira ga gwamnatin tarayya

Jaridar tace a jawabin da Gwamna Diri ya gabatar, ya yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya ta sa dokar ta-baci kan lamarin ambaliya.

Bayelsa
Gidan Gwamnatin Bayelsa Hoto: Khalid' Ozavogu Abdul
Asali: Twitter

Kamar yadda Gwamnan na jihar Bayelsa ya fada a taron da aka yi a karshen makon da ya wuce, ambaliyar shekarar nan ya yi barna kwarai da gaske.

Douye Diri yace barnar da ruwa ya yi a bana, har ya zarce abin da aka gani a shekarar 2012. Wannan rahoto ya zo a jaridar Daily Post a ranar Lahadi.

Dalibai ba za su koma makaranta ba

"Yanzu haka da muka magana, kungiyar ASUU ta janye yanjin-aikinta. Yayin da ake bude jami’o’i, ba za a iya bude jami’ar jihar mu ba.
Dalilin wannan kuwa shi ne titin zuwa jami’ar nan ya gutsure, ya rabu uku.
Titin da ya hada Opokuma da Sabagreia a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma da hanyar Sagbama zuwa Ekeremor da ake yi, duk sun karye."

- Gwamna Douye Diri

Gwamnan yace mutane sun shiga wani mummunan hali na yunwa da tashin hankali a jiharsa.

Za a kai agaji zuwa jihohi

A sakamakon halin da ake ciki, an samu rahoto Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yarda a raba kayan abinci a wuraren da ake fama da ambaliyan ruwa.

Ambaliyan bana ya shafi jihohi 27, don haka gwamnatin tarayya take bada agajin gaggawa, amma tace akwai laifin mutanen da ke rayuwa a wuraren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng