Tashin Hankali Yayin da Wani Hadari Ya Lakume Rayukan Mutane Sama da 10 a Bauchi

Tashin Hankali Yayin da Wani Hadari Ya Lakume Rayukan Mutane Sama da 10 a Bauchi

  • Wani mummunan haɗarin Mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 11 yayin da wasu Takwas suka jikkata a jihar Bauchi
  • Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra a Bauchi, Yusuf Abdullahi, yace Motoci dauke da mutane 20 ne haɗarin mara kyau ya rutsa da su
  • Mista Abdullahi ya alaƙanta abinda ya jawo haɗarin da Tuki mai haɗari inda ya nemi matafiya su kula ɗa ka'idojin hanya

Bauchi - Wani Ibtila'i ya auku a kauyen Hawan Jaki da ke Titin Alkaleri-Gombe a ƙaramar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi ranar Asabar yayin da mutane 11 suka mutu a haɗarin mota.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) na yankin Bauchi, Mista Yusuf Abdullahi, ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) cewa wasu mutum 8 sun jikkata sakamakon haɗarin.

Kara karanta wannan

Yadda Zan Tsaya Na Yaki Yan Bindiga Idan Na Zama Shugaban Kasa a 2023, Tinubu

Jami'an hukumar kiyaye haɗurra.
Tashin Hankali Yayin da Wani Hadari Ya Lakume Rayukan Mutane Sama da 10 a Bauchi Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Yace hatsarin ya rutsa da wata Motar haya ta kamfanin Yankari Express da kuma wata Motar Ɗangote, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Menene ya haddasa haɗarin?

Mista Abdullahi ya jingina musabbabin abinda ya jawo hatsarin da mummunna tuƙi mai haɗari, inda yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Maza matasa 20 ne mummunan haɗarin ya rutsa da su, mutum Tara daga ciki suka mutu nan take a wurin yayin da Likitoci suka tabbatar da cikawar wasu biyu a babban Asibitin Alkaleri."
"Haka nan wasu mutum Takwas sun ji raunuka iri daban-daban kuma yanzu haka suna kwance a Asibitin Alkaleri ana kulawa da lafiyarsu. Jami'ai sun kai gawarwakin wadanda suka Mutu asibitin."

Kwamadan FRSC, Mista Abdullahi, ya kara da gargaɗin matafiya cewa a ko da yaushe su rika kokarin kiyayen ƙa'idoji da dokokin tuki yayin da suka hau kan titi, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗan Fitaccen Ɗan Majalisar Arewa, Sun Kashe Jami'in Tsaro

A wani labarin kuma Gwamnan Bauchi Ya Umarci Ciyamomi 20, Mataimaka da Wasu Kusoshin Gwamnati Su Sauka Daga Kujerunsu

Gwamna Bala Muhammed na Bauchi ya umarci Ciyamomi 20 su sauka daga kujerunsu bayan wa'adinsu ya ƙare.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar, umarnin ya shafi mataimakan ciyamomi, Sakatarori da Kansiloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262