Gwamnatin Tarayya Kadai Ba Za Ta Iya Rike Jami'o'i Ba, Iyaye Ya Kamata Su Fara Tallafawa, Inji Gwamna Inuwa

Gwamnatin Tarayya Kadai Ba Za Ta Iya Rike Jami'o'i Ba, Iyaye Ya Kamata Su Fara Tallafawa, Inji Gwamna Inuwa

  • Jim kadan bayan da ASUU ta ayyana janye yajin aiki, gwamnan jihar Gombe ya bayyana wani batu mai daukar hankali
  • Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce akwai bukatar iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su mai da hankali tare da shuga lamarin jami'o'in kasa
  • Kungiyar ASUU ta shafe watanni tana yajin aiki, a yau Juma'a 14 ga watan Oktoba ne ta sanar da janye yajin

Jihar Gombe - Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya kadai ba ta da karfin iya rike jami'o'in kasar, Channels Tv ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar iyaye da sauran masu ruwa da tsaki suke shiga lamarin domin tabbatar da tafiyar da makarantu cikin kwanciyar hankali.

Gwamnan Gombe ta ce jami'o'i sun fi karfin gwamnati, dole iyaye su kawo dauki
Gwamnatin Tarayya Kadai Ba Za Ta Iya Rike Jami'o'i Ba, Iyaye Ya Kamata Su Fara Tallafawa, Inji Gwamna Inuwa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Juma'a jim kadan bayan da kungiyar ASUU ta ayyana janye yajin aikin da ta shafe watanni takwasi tana yi a kasar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

Ya kuma bayyana cewa, matsalar da ASUU ke fuskanta bata samu mafita na dindindin ba, don haka ya kamata gwamnati da al'umma su nemo hanyar da ta dace wajen warware damuwar baki daya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, ya kuma ga caccaki tsohuwar gwamnatin kasar nan da shiga yajejeniyar da ba za ta warware ba tsakaninta da kungiyar ta malaman jami'a.

A cewarsa, tun farko gwamnatin baya ta san ba za ta iya cika alkawuran da ta daukarwa ASUU ba, amma a haka ta tafi da yarjejeniyar da babu gaskiya a cikinta.

Daga nan ne ya bukaci masu ruwa da tsaki, kungiyoyi, iyaye da sauran al'umma da su shigo lamarin jami'a a Najeriya domin kawo karshen irin wadannan matsaloli na yajin aiki.

Abu biyu da zai faru, ini malamar jami'a

Legit.ng Hausa ta tattauna da wata malamar jami'ar jiha ta Gombe, Aisha Usman Muhammad ta bayyana hasashenta game da maganar gwamna Yahaya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Nnamdi Kanu, Ta Umurci Gwamnati Ta Sake Shi

Ta bayyana cewa:

"A matsyinmu na malamai dai munyi kokarin muga baa kai wannan matakin ba. Amma idan gwamnati ta saka wannan dokan babu yadda aka iya. Illa dai karatun jamia zai gagari talaka.
"Tallafin da iyaye zasu biyar shine biyan kudin makaranta kamar yadda ake biya a jami'o'i masu zaman kansu.
"Sai kuma masu kudi zasu iya bada tallafi da kudaden gudanar bincike ga jami'o'in."

ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

A wani labarin, kungiyar Malamai ta Jami’o’i ASUU ta janye yajin aikinta da ta kwashe tsawon wata takwas tana yi.

Sai dai a takardar da kungiyar ta fitar kuma jaridar Punch ta gani, tace har yanzu da suna cikin rikici da gwamnatin tarayyya kuma ba a shawo kan bukatunsu ba.

Takardar da aka saki ga manema labarai wacce ta samu da hannun shugaban kungiya, Farfesa Emmanuel Osodeke, ta yabawa ruwa da tsakin da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yayi wirin shawo kan matsalar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Hukuncin Babban Kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.