Gwamnatin El-Rufa'i Ta Shirya Wa Sabbin Ma'aikata 10,000 Jarabawa, Ta Fadi Ranaku
- Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya gwaji ga sabbin malaman makaranta 10,000 da take gab da ɗauka aiki
- Hukimar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar, (KADSUBEB), a wata sanarwa tace Malaman za su zana jarabawar a tsakanin 17 zuwa 28 ga Oktoba
- Shugaban hukumar, Malam Tijani Abdullah, ya ce gwamna Malam El-Rufai ya umarci su ɗauki sabbin malamai 10,000
Kaduna - Hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna, (KADSUBEB), tace ta shirya tsaf don gudanar da jarabawa ga sabbin malaman makaranta da zata ɗauka aiki.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hukumar ta sanya ranakun 17 zuwa 28 ga watan Oktoba, 2022 a matsayin lokacin zama jarabawar a shiyyoyin jihar guda uku.
A wata sanarwa da KADSUBEB ta fitar, ta ce a shiyyar kudancin Kaduna, jarabawar zata gudana a makarantar Institute of Information Technology, Kofar Doka, Zaria.
Haka zalika a Kaduna ta tsakiya jarabawar zata gudana ne a Jami'ar jihar Kaduna (KASU) dake cikin birnin Kaduna, yayin da reshen KASU da ke Kafanchan zai wakilci shiyyar kudancin Kaduna.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A watan Yuli da ya gabata, Shugaban hukumar KADSUBEB, Malam Tijani Abdullah, ya ce gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna ya umarci hukumar ta ɗauki sabbin malamai 10,000.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tun a zangon Mulkin Gwamna El-Rufai na farko, gwamnatin ta kori Malaman makaranta da dama bayan sun faɗi jarabawar gwaji.
Lamarin dai ya haifar da cece-kuce daga sassan jihar, inda wasu ke ganin ya kamata gwamnan ya biya Malaman hakkokinsu kafin ya sallame su.
Alkawurran da FG ta ɗaukarwa ASUU
A wani labarin kuma Gwamnati Za Ta Baiwa Malaman ASUU N50bn Kudin Alawus, N170bn Kudin Karin Albashi
Bayanai sun fara fitowa game da alkawuran da gwamnati ta yiwa kungiyar malaman jami'a ASUU.
Ana kyautata zaton dai ASUU zata janye daga yajin aikin biyo bayan shiga tsakani da Kakakin majalisa yayi.
Asali: Legit.ng