An Ware Sheikh Isa Pantami Shi Kadai, An ba shi Kyautar Kasar Waje a Birnin Dubai

An Ware Sheikh Isa Pantami Shi Kadai, An ba shi Kyautar Kasar Waje a Birnin Dubai

  • An karrama Isa Ali Ibrahim Pantami a wani taro da ake yi a birnin Dubai da ke United Arab Emirates
  • Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamanin ya tashi da kyautar DWTC na shekarar 2022
  • A matsayinsa na shugaban WSI Process, Ministan Najeriyan kadai ya samu wannan lambar yabo

UAE - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu lambar yabo saboda kokarin da yake yi a ofis.

Kamar yadda ya bayyana a Twitter a ranar Talata, 11 ga watan Oktoba 2022, Mai girma Ministan ya tashi da kyautar DWTC a Dubai a kasar UAE.

An ba Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami wannan lambar yabo ne la’akari da ayyukan da yake yi wa Najeriya tun da ya zama Ministan sadarwa a 2019.

Kara karanta wannan

Mutane 4 da Aka Taba Ba Su Lambar Yabo, Amma Suka Ki Karba a Tsawon Shekaru 58

Jaridar Science Nigeria tace an karrama Isa Pantami bayan ya gabatar da jawabinsa a game da yadda za a tafi da kowa a harkar sadarwa na zamani.

Pantami ya yi jawabin ne a taron GITEX wanda ake yi yanzu haka a dunkullaliyar kasar Larabawa.

Rahoton yace Ministan ya dauki lokacinsa yana mai bayanin nasarorin da ya kawowa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar bunkasa bangaren ICT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Isa Pantami
Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

A cewar Ministan, za a raba kokarin da suka yi zuwa gida biyu; ilmantar da al’umma a kan fasahohin zamanin da kuma samar da damammaki ga mutane.

Isa Pantami yace gwamnatin tarayya ta fito da tsarin NDEPS wanda ya taimaka wajen ganin 'yan Najeriya sun samu ilmi da dama a harkar zamanin.

Kamar yadda ya fada shafinsa na Twitter, malamin addinin kuma masani a kan harkar, yace har zuwa ranar (Talata), shi kadai aka ba lambar yabon.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar LP Ta Fitar Sunayen Mambobi 1,234 Na Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa, Babu Jiga-Jigai 2

Kyauta daga kasar waje

"Farfesa Pantami ya tashi da lambar yabo na kasar waje
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, @ProfIsaPantami ya samu kyautar shugabanci na GITEX
Ya lashe kyautar ne la’akari da kokarin da ya yi da jajircewarsa wajen bunkasa tattalin arzikin zamani.
Mutumin da zuwa yanzu, shi kadai aka karrama da wannan kyauta a shekarar nan, shugaban @WSISprocess."

- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami

Rahoton ya nuna tsohon malamin jami’ar ya ji dadin samun wannan kyauta, yace lambar yabon ta nuna nasarorin da bangaren ICT ya samu a karkashinsa.

Mun yi ayyuka 2000 - Pantami

Kwanaki an ji labari Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi bayanin irin nasarorin da ya samu a tsawon shekaru uku a ofis.

Da yake magana da ya kai wata ziyara a Abuja, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ba mutane shawarar su samu horo na ICT domin samun aiki a kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Za'a magance dukkan matsalolin tsaron Najeriya nan da watan Disamban, Gwamnati

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng