Zamfara: ‘Yan sanda Sun Kama Mota Dankare da Kayan Abinci da Miyagun Kwayoyi Za a Kaiwa ‘Yan Bindiga
- Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun kama babbar mota dankare da kayan abincin da za a kai wa ‘yan bindiga maboyarsu dake Dangulbi
- Kamar yadda kakakin rundunar na jihar Zamfara ya sanar, an kama mutum takwas dake kai wa ‘yan bindiga bayanai, harsasai 250 da shanun sata 47
- A babbar motar an samu miyagun kwayoyin tramadol, exzol, alluran Penta da Chloroquine, kwalayen giya da atamfofi biyu daga hannun direban
Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun kama mota dankare da kayan abinci da za a kaiwa ‘yan bindigan dake da maboya a Dangulbi a karamar hukumar Maru ta jihar, jaridar Premium Times ta rahoto.
A wata takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu yasa hannu a ranar Laraba, ‘yan sandan sun damke mutum takwas dake kai wa ‘yan bindiga bayanai, harsasai carbi 250 na AK47 da shanun sata 47.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwayoyin da aka samu
An kama direban babbar motar yayin da yake kana hanyar kai wa ‘yan bindiga abinci a Maru, Anka da Gusau dake yankin dajin Dangulbi da Magami.
“Miyagun kwayoyin sun hada da allurar Penta, kwayoyin tramadol, allurorin chloroquine, kwayoyin exzol da kwalayen giya. An samu turamen atamfofi biyu duk a motar.”
- Kakakin rundunar ‘yan sandan yace.
An kama bindigu daga wasu wadanda ake zargi
Mutum biyu masu suna Hauwa Usman da Aliyu Mamuda an kama su a dajin Munhaye dake karamar hukumar Tsafe. Sun amsa cewa sune ke kai wa ‘yan bindiga kayan abinci a dajin Munhaye.
Kakakin rundunar ‘yan sandan yace sauran mutum biyun dake kai bayanai an kama su ne a yankunan kananan hukumomin Gusau da Maru.
An kama wasu mutum biyu masu suna Musa Umar da Idris Yaro an kama su da shanun sata tara a kan titin Magami da Wanke a Gusau.
Dakarun Sojin Najeriya sun Kama Wiwi ta N4m wacce Za a Kai wa ‘Yan Ta’adda a Yobe
A wani labari na daban, dakarun sojin sashi na biyu na Operation Hadin Kai a jihar Yobe sun sanar da kama wata wiwi mai tarin yawa da ake zargin an nufi kai ta maboyar ‘yan ta’adda ne a iyakar Najeriya da Nijar, jaridar The Nation ta rahoto.
Shugaban ma’aikatan sashi na biyu na kwamandan Operation Hadin Kai, Birgediya Janar Umar Muazu a jiya ya mika kayayyakin da suka kwace zuwa Hukumar Yaki da Fasakwabrin Miyagun Kwayoyi a hedkwatarsu ta Damaturu.
Asali: Legit.ng