Mutane 4 da Aka Taba Ba Su Lambar Yabo, Amma Suka Ki Karba a Tsawon Shekaru 58
Abuja - Daga lokacin da aka soma bada lambar karramawar zuwa yau, akwai fitattun mutane da suka ki amincewa da lambobin da gwamnati ta ba su
A shekarar 1964 aka fara raba lambar girma, a lokacin Alhaji Tafawa Balewa yana Firayim Ministan Najeriya, har yanzu an cigaba da wannan al'ada
Legit.ng ta bi tarihi, ta iya kawo sunayen irinsu Farfesa Chinua Achebe, Alhaji Gidado Idris da kuma Gani Fawehinmi, wanda sun yi fatali da shaidar girman
1. Chinua Achebe
Sau biyu Farfesa Chinua Achebe ya yi watsi da lambar yabo. An yi haka a 2004 da 2011 yayin da Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan suke mulki.
Marubucin ya yi hujja da cewa bai gamsu da yadda abubuwa suke tafiya a kasar ba, don haka ya ki karbar lambar girman domin ya nuna fushinsa a fili.
Shekaru kusan biyu bayan ya ki karbar lambar CFR, wannan fitaccen marubuci ya bar Duniya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
2. Gidado Idris
A shekarar 2008. Gwamnatin Umaru Musa Yar'Adua ta nemi ta ba Alhaji Gidado Idris lambar CFR, amma ya nuna bai da sha’awa, ya kuma bada dalilinsa.
Tsohon sakataren gwamnatin kasar yace Janar Abdusalam Abubakar ya ba shi shaidar GCON, don haka karbar lambar a lokacin zai bada wata ma’ana dabam.
3. Gani Fawehinmi
Gani Fawehinmi gawurtaccen Lauya ne mai kare hakkin Bil Adama wanda ya ki karbar lambar OFR a lokacin da gwamnatin Yar’Adua ta nemi ta karrama shi.
Kamar yadda ya fada a shekarar 2008, Najeriya tana fama da matsalar shugabanci na kwarai, saboda haka ya ki amsar lambar yabon gwamnatin tarayya mai-ci.
4. Femi Gbajabiamila
A lokacin yana shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Hon. Femi Gbajabiamila ya ki amincewa ya karbi OFR a hannun Goodluck Jonathan.
2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya
Bayan shekaru 11 sai Gbajabiamila ya karbi lambar daga wajen Muhammadu Buhari. A 2011 ‘dan majalisar yace gwamnati ta karrama mutanen da ba na kwarai ba.
Mutum 420 sun samu lambar girma
Ku na da labari Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama mutum fiye da 400 a Najeriya da lambar girmamawa a makon nan a birnin tarayya Abuja.
Shugabar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala; Ishaq Oloyede na JAMB da Ministocin tarayya irinsu Babatunde Fashola da Adamu Adamu sun samu lambar girma.
Asali: Legit.ng