Mamaki Yayin Da Gwamnatin Buhari Ta Amince EFCC Ta Gurfanar Ta Shahararriyar Sanatan APC A Kotu

Mamaki Yayin Da Gwamnatin Buhari Ta Amince EFCC Ta Gurfanar Ta Shahararriyar Sanatan APC A Kotu

  • EFCC za ta gurfanar da sanata Stella Adaeze Oduah a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja a watan Fabrairun 2023
  • Antoni Janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, SAN, ne ya bada amincewar a gurfanar da Sanata Odu'ah a ranar Laraba 12 ga watan Oktoba
  • Za a gurfanar da Oduah da wasu mutane ne kan zargin almundahar kudi fiye da Naira Biliyan 7.9

Abuja - An amincewa Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da Sanata Stella Adaeze Oduah ta jam'iyyar All Progressives Congress, APC, kan zargin almundahar kudi fiye da N7.9 biliyan.

Ministan shari'a kuma Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami, SAN, ne ya bada amincewar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Buhari
Mamaki Yayin Da Gwamnatin Buhari Ta Amince EFCC Ta Gurfanar Ta Shahararriyar Sanatan APC A Kotu. Hoto: Aso Rock Villa.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Mutane 4 da Aka Taba Ba Su Lambar Yabo, Amma Suka Ki Karba a Tsawon Shekaru 58

Umurnin da Malami ya bawa hukumar, ya kuma bawa babban kotun tarayya da ke Abuja, hakan ya kawo karshen yawaita fara sauraron karar da ya janyo gurfanar da Sanata Oduah.

Yayin zaman kotu a ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba, an bawa yar majalisar da sauran wadanda za a gurfanar da su tare ranar 13, 14, 14, 15, 16 da 17 na watan Fabrairun 2023, don gurfanarwa kamar yadda Mai shari'a Inyang Ekwo ta karanto.

Tuhume-tuhumen da aka yi wa Stella Oduah

Oduah, kamar yadda ya ke cikin karar da EFCC ta shigar, ta bannatar da N7.9 biliyan na kudin gwamnati a yayin da ta ke ministan harkokin sufurin jiragen sama karkashin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Laifukan da ake tuhumarta da aikatawa sun hada da hadin baki, karkatar da kudade, da mallakar asusun bankuna na 'boye'.

Wadanda aka yi kararsu tare da Oduah sun hada da Gloria Odita, Nwosu Emmanuel Nnamdi, Chukwuma Irene Chinyere, Global Offshore, Marine Limited, Tip Top Global Resources Limited, Crystal Television Limited, da Sobora International Limited.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar LP Ta Fitar Sunayen Mambobi 1,234 Na Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa, Babu Jiga-Jigai 2

EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa

A wani labarin, mun kawo muku cewa Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa Premium Times cewa a halin yanzu jami'an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164