Da Duminsa: Buhari ya Rantsar da Jastis Ariwoola Matsayin Alkalin Alkalan Najeriya

Da Duminsa: Buhari ya Rantsar da Jastis Ariwoola Matsayin Alkalin Alkalan Najeriya

  • Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Ariwoola Olukayode matsayin alkalin alkalan Najeriya
  • Kamar yadda Buhari Sallau ya bayyana, an bashi rantsuwar ne a fadar shugaban Kasa Muhammadu Buhari a takaitaccen biki a Abuja
  • A zantawarsa da manema labarai, Mai shari’a Ariwoola yayi kira ga ‘yan siyasa da su basu damar aikinsu yayin da zaben 2023 ke gabatowa

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Ariwoola Olukayode matsayin tabbata ne alkalin alkalan Najeriya.

Ariwoola Olukayode
Da Duminsa: Buhari ya Rantsar da Jastis Ariwoola Matsayin Alkalin Alkalan Najeriya. Hoto daga @Buharisallau1
Asali: Twitter

Mai shari’a Ariwoola ya karba rantsuwar kama aiki a ranar Laraba a takaitaccen bikin da aka yi a fadar shugaban kasa dake Abuja kafin fara taron mako-mako na majalisar zartarwar Najeriya wanda shugaban kasan yake jagoranci.

Kara karanta wannan

Kallon Mamakin da Buhari Yayi wa Shigar Ezra Olubi a Wurin Bada Lambar Yabo ya Janyo Cece-kuce

Shagalin ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ministoci da sauran alkalan kotun koli, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An zabi mai shari’a Ariwoola matsayin alkalin kotun koli a ranar 22 ga watan Nuwamban 2011 a zamanin mulkin shugaba Goodluck Jonathan.

A wata zantawa da manema labarai, alkalin alkalan yayin kira ga ‘yan siyasa a kasar nan da su bar fannin shari’a yayin aikinsa yayin da zaben 2023 ke gabatowa inda ya sha alwashin kawo sauye-sauye a kotun jikin.

Bayan murabus din Mai shari’a Tanko Muhammad kan batun lafiyarsa, mai shari’a Ariwoola ya karba ragamar kotun matsayin mukaddashi.

Gaskiya Tayi Halinta: Yadda Aka Tirsasa CJN Tanko Yayi Murabus Kan Dole

A wani labari na daban, murabus din alkalan alkalan Najeriya, Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad a ranar Litinin ya biyo bayan wasu manyan fadi-tashi da aka dade ana shiryawa amma aka kaddamar da su a daren Lahadi, majiyoyi da dama da suka san kan lamarin suka tabbatar wa da Daily Trust.

Kara karanta wannan

Za'a magance dukkan matsalolin tsaron Najeriya nan da watan Disamban, Gwamnati

Majiyoyi masu karfi sun ce akasin tunanin da ake na cewa Muhammad yayi murabus da kansa ne, tirsasa shi aka yi daga cikin manyan jami'an tsaro da jami'an gwamnati.

Bayan murabus dinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari'a Olukayode Ariwoola, na biyu a daraja a kotun kolin, a matsayin mukaddashi alkalin alkalan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng