Dakarun Sojin Najeriya sun Kama Wiwi ta N4m wacce Za a Kai wa ‘Yan Ta’adda a Yobe
- Zakakuran sojojin rundunar Operation Hadin Kai dake Yobe sun kama wiwi mai darajar N4 miliyan da za a kai wa ‘yan ta’adda
- Kamar yadda shugaban ma’aikatan sashi na 2 na rundunar dake Yobe ya sanar, wadanda suka dauko wiwin sun nufi Tungus ne amma suna ganin sojoji suka bar ababen hawansu tare da tserewa
- Tuni dakarun suka kwashe sunki 98 na wiwin suka mika hannun hukumar NDLEA dake jihar Yobe hannun mataimakin kwamandan su Peter Ogar
Yobe - Dakarun sojin sashi na biyu na Operation Hadin Kai a jihar Yobe sun sanar da kama wata wiwi mai tarin yawa da ake zargin an nufi kai ta maboyar ‘yan ta’adda ne a iyakar Najeriya da Nijar, jaridar The Nation ta rahoto.
Shugaban ma’aikatan sashi na biyu na kwamandan Operation Hadin Kai, Birgediya Janar Umar Muazu a jiya ya mika kayayyakin da suka kwace zuwa Hukumar Yaki da Fasakwabrin Miyagun Kwayoyi a hedkwatarsu ta Damaturu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Muazu yace wanda ke dauke da wiwin ya yasar da ita tare da tserewa bayan ya hango dakarun dake sintiri.
Muazu yace an yi nufin kai miyagun kwayoyin ne Tungus, wata maboyar ‘yan ta’adda dake iyakar Najeriya da Nijar.
“Babu wanda ake zargi da aka kama saboda dukkansu sun bar ababen hawansu sun tsere bayan da suka hango tawagar sintiri suna kokarin kama su.
“Zasu kai kayayyakin ne maboyar ‘yan ta’adda saboda wadannan abubuwan ne suke sha suna yin abinda suka so na barna saboda babu mutum mai cikakken hankali da zai yi abinda suke yi ba tare da sun bugu ba.
“A yanzu mun kwace wannan kuma da izinin Allah muna cigaba da matsantawa ‘yan ta’addan a yankin arewa maso gabas.”
- Muazu yace.
A jawabinsa bayan karbar kayayyakin, Peter Ogar, mataimakin kwamandan NDLEA na jihar Yobe a madadin hukumar ya mika godiyarsa ga sojojin kan hadin kan da suka dabbaka tsakaninsu da sauran hukumomin tsaro.
Ya sanar da manema labarai cewa, sunki 98 na miyagun kwayoyin suna da daraja a kasuwa wacce ta kai N4 miliyan.
Hotuna da Bidiyon Sojan Dake Satar Makamai Yana Kaiwa ‘Yan Bindiga Yayin da Dubunsa ta Cika
A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta damke wani soja da ake zargi da satar makamai tare da kaiwa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.
Kamar yadda kwararre a kiyasin tsaro, Zagazola Makama ya bayyana a shafinsa na Twitter, yace sojan mai suna Iorliam Emmanuel dubunsa ta cika.
‘Dan asalin jihar Binuwai din yana aiki ne da 156 Task Force Battalion dake Mainok a jihar Borno a karkashin rundunar Operation Hadin Kai.
Asali: Legit.ng