AEDC ta Gutsure Wutar Lantarkin Gidan Gwamnatin Niger Kan Bashin N1.8b

AEDC ta Gutsure Wutar Lantarkin Gidan Gwamnatin Niger Kan Bashin N1.8b

  • Kamfanin Rarrabe Wutar Lantarki na Abuja, AEDC ya yanke wutar gidan gwamnatin jihar Niger kan bashin N1.8 biliyan na wutar lantarki da ake bin su
  • Manyan wuraren da aka yankewa wutar suna hada da majalisar jihar, babban asibitin Minna, asibitin IBB, gidan ruwa da sakateriyar gwamnatin jihar
  • Mai magana da yawun AEDC, Mohammed Auwal, ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace suna taro don haka ba zai yi tsokaci a kai ba

Niger - Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja, AEDC, ta gutsure wutar lantarkin gidan gwamnatin jihar Niger, wutar majalisar jihar da ta babban asibitin Minna da sauransu kan bashin da ake bin su.

Niger Governor
AEDC ta Gutsure Wutar Lantarkin Gidan Gwamnatin Niger Kan Bashin N1.8b. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Sauran manyan wuraren da ake yankewa wutar sun hada da asibitin kwararru na IBB, gidan ruwa na jihar da sakateriyar jihar.

Kara karanta wannan

2023: Kusoshin Kiristocin Jam’iyya Za Su yi Taron Dangi Domin Dankara Tinubu da Kasa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan shi ne karo na uku da aka yankewa gidan gwamnatin jihar wutar lantarki a wannan shekarar sakamakon yadda suka kasa mutunta yarjejeniyar dake tsakaninsu tun a watan Augusta na biyan kudin da ake bin su.

Idan za a tuna, AEDC ta fara yanke wutar cibiyoyin gwamnatin a ranar 20 ga watan Afirilu kuma ta sake yankewa a ranar 26 ga watan Augusta.

A yayin rubuta wannan rahoton, ba a mayar da wutar ofisoshi da sassa da yawa na jihar ba.

An ga jami’an AEDC da tsanika suna kaiwa da kawowa a wurin ofisoshin domin yanke wutar, jaridar Vanguard ta rahoto.

AEDC tace gwamnati ta ki cika sharadin da aka gindaya mata na biyan bashin sama da N1.8 biliyan kamar yadda ta amince kafin a mayar musu da wuta a watan Augusta.

Kara karanta wannan

Ba harka: Dan takarar shugaban kasan wata jam'iyya ya tsorata, zai janye daga takara

Mai magana da yawun AEDC na jihar Niger, Mohammed Adamu, ya tabbatar da yanke wutan.

“Wannan abun gaskiya ne amma muna taro ne don haka ba zan iya bada karin bayani ba.”

- Yace.

An Yanke Wutan Gidan Gwamnati da Ofisoshi Saboda Rashin Biyan Kudin Lantarki

A wani labari na daban, Kamfanin Abuja Electricity Distribution Company watau AEDC masu raba wutar lantarki a jihar Neja sun datse wutar ma’aikatun gwamnati.

Jaridar Daily Nigerian tace hakan ya biyo bayan tulin bashi da kamfanin na AEDC yake bin gidan gwamnati, ma’aikatu da hukumomin jihar ta Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng