Rikicin Mallaka: Dangote da Yahaya Bello Sun Gurfana a Fadar Buhari Za a Yi Musu Sasanci
- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da Alhaji Aliko Dangote, shugaban kamfanonin Dangote sun garzaya fadar Buhari don sasanci
- Sun fara ganawa wurin karfe 4 na yammacin Litinin inda shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari ya halarta gare da Gwamna Abdullahi Sule
- Wannan dai ya biyo bayan rikicin da yasa gwamnatin Kogi ta garkame kamfanin simintin kan zargin Dangote da mallaka filayen wurin ba bisa ka'ida ba
FCT, Abuja - Alhaji Aliko Dangote, shugaban kamfanonin Dangote a ranar Litinin ya halarci wata ganawa tare da Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a fadar shugaban kasa.
Taron wanda ya samu halartar Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa an yi shi ne domin rikicin mallakin kamfanin simintin Dangote dake Obajana a jihar Kogi, jaridar TheCable ta rahoto.
TheCable ta gano cewa an fara taron ne da karfe hudu na yammacin ranar Litinin.
Wannan cigaban na zuwa ne bayan kwanaki da majalisar jihar Kogi tayi umarnin rufe kamfanin Dangote bayan asalin 'yan yankin sun tada balli kan batun mallakar kamfanin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai a yayin yunkurin rufe kamfanin simintin a ranar 5 ga watan Oktoba, an yi harbe-harben bindiga amma daga bisani an rufe kamfanin.
Sai dai babu tabbacin mutum nawa aka harba yayin da shugabannin yankin suka yi Allah wadai da shigar matasan yankin cikin rikicin wanda hakan ya janyo harbin.
A daya bangarne, gwamnatin jihar Kogi ta kafa kwamiti domin ya duba yadda Dangote ya mallaki filin da aka yi kamfanin simintin inda kwamitin ya tabbatar da cewa an yi shi ba bisa ka'ida ba.
Kudin da kamfanin simintin Dangote PLC ya samu a shekarar 2021 ya zarce N1.02tr
A wani labari na daban, kamfanin Dangote Cement Plc wanda shi ne babban kamfanin siminti a fadin Afrika, ya fito da rahoton kudi da ribar da ya samu a shekarar nan.
Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, 2021, cewa abin da kamfanin mai fitar da 48.6Mta a duk shekara, yake samu, ya karu.
Alkaluma sun nuna kamfanin ya samu Naira tiriliyan 1.02 daga watan Junairu zuwa Satumban bana. Bayan cire haraji, an samu ribar Naira biliyan 405.5.
Asali: Legit.ng