Nan da Kwanaki Kadan Za a Janye Yajin Aikin ASUU, Lauyan ASUU Falana Ya Magantu
- Babban lauya a Najeriya ya bayyana cewa, nan ba da jimawa kungiyar malaman jami'a za su janye yajin aiki
- Femi Falana, wanda kuma shine lauyan ASUU ya ce, kungiyar za ta koma bakin aiki cikin 'yan kwanaki kadan
- Kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta shiga yajin aiki tun watan Fabrairun bana saboda gwamnati ta ki biya mata bukata
Jihar Legas - Babban lauya Femi Falana ya bayyana kwarin gwiwar cewa, nan ba da dadewa kungiyar malaman jami'a karkashin ASUU za su janye yajin aikin da suke yi tun watan Fabrairun bana.
Falana ya bayyana cewa, janye yajin aikin ba wai makwanni zai dauka ba, zai zo ne cikin 'yan kwanaki masu zuwa nan kusa, rahoton Tribune Nigeria.
Babban lauyan ya bayyana hakan ne a yau Litinin 10 ga watan Oktoba a jihar Legas yayin bikin kaddamar da littafi mai suna Breaking Coconut With Your Head da Lanre Arogundade ya wallafa.
Ya kuma bayyana cewa, akwai yiwuwar dinke duk wata baraka ta yajin aikin a wajen kotu, kamar yadda aka ba kungiyar shawari.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ba Zan Sake Shiga Yarjejejiya da ASUU Ba, Shugaba Buhari Ya Magantu
A makon jiya, shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya yiwa kungiyoyin jami'o'in kasar bayani, ya ce ba zai yi musu alkawarin da ba zai iya cikawa ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a martaninsa ga kungiyar malaman jami'a ta ASUU dake yajin aiki tun watan Fabrairun bana, Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai, shugaban ya ce gwamnati na rike da alkawuran da ta dauka kuma ta rubuta yarjejeniya da ASUU a baya.
Buhari ya ce, a yanzu dai gwamnati kadai ba za ta iya daukar nauyin dukkan bukatun jami'o'in kasar nan ba.
A wani labarin, kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) za ta tunkari kotun ma'aikata kan lamarin da gwamnati ta gabatar na yiwa kungiyoyin dake kishiyantarta rajista.
Lauyan ASUU, Femi Falana ne ya shaidawa Channels Tv cewa, kungiyar za ta tunkari kotun ma'aikata domin kai kokenta.
Hakazalika, shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a ranar Alhamis 6 ga watan Okotoba.
Asali: Legit.ng