Gwamna Matawalle Ya Gwangwaje Makarantun Islamiyyun Zamfara da Sha Tara da Arziki

Gwamna Matawalle Ya Gwangwaje Makarantun Islamiyyun Zamfara da Sha Tara da Arziki

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta ba da tallafin shanu 97 da buhunan shinkafa 199 ga makarantun koyon karatun Alkur'ani na jihar
  • Kwamishinan harkokin addinai na Zamfara, Dakta Tukur Sani Jangebe, yace an yi haka ne domin tallafa musu su yi bikin Maulidi
  • Ya kuma taya ɗaukacin Al'ummar Musulmai murnar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW)

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta raba buhunam Shinkafa 199 da Shanu 97 ga Makarantun haddar Alƙur'ani dake faɗin sassan jihar ta arewa maso yammacin Najeriya.

Kwamishinan ma'aikatar harkokon Addinai, Dakta Tukur Sani Jangebe, shi ne ya bayyana haka, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Tambarin Gwamnatin jihar Zamfara.
Gwamna Matawalle Ya Gwangwaje Makarantun Islamiyyun Zamfara da Sha Tara da Arziki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jangeɓe, wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma'aikatar Addinai, Sani Nasarawa, a wurin kaddamarwa, yace tallafin ya fito ne daga gwamna Bello Matawalle..

Kwamishinan yace tallafin wani karamci ne daga mai girma gwamna Matawalle zuwa ga Makarantun Alƙur'ani domin su yi murnar haihuwar fiyayyen Halitta tsira da amincin Allah su daɗa tabbata a gare shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Dan Siyasa Kuma Na Kusa da Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Rasu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna rokon ɗaukacin Malamai su sanya jihar Zamfara da ƙasa baki ɗaya a addu'o'insu musamman lokaci irin waɗannan masu daraja," inji shi.

Bugu da ƙari, Kwamishinan harkokin addinai ya taya ɗaukacin al'ummar Musulmai murnar zagayowar Maulidin Manzon Allah (SAW).

Haka zalika ya yi kira ga mutane su rungumi zaman lafiya sannan kuma su nuna wa junansu soyayya ba tare da duba asali, Addini ko ƙabila ba.

Mutane sun yi wa gwamnan Jigawa Ihun Bamayi

A wani labarin kuma Mutane Sun Yi Wa Gwamnan Badaru Ihu a Wurin Bikin Maulidin Annabi SAW

Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya halarci bikin al'ada da aka saba shiryawa duk shekara a Masarautar Gumel lokacin Maulidi.

Sai dai mutane da basu ji dadin halin da gwamnan ya nuna game da Ambaliyar ruwa ba sun masa ihun 'Bamayi Bamayi'.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Kwankwaso? An Bayyana Dan Takarar Da Ya Shirya Ceto Najeriya Idan Ya Gaji Buhari a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel