Hotunan Buhari Yayin da ya Ziyarci Ragowar Fasinjojo 23 na Jirgin Kasa da Boko Haram Suka Saki
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci fasinjoji 23 na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da suka samu ‘yanci
- Kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana, Buhari ya ziyarcesu a asibitin NDA inda ya yabawa sojojin
- Ya gana da fasinjojin tare da taya su murnar iskar ‘yancin da suka samu bayan kwashe watanni shida a hannun ‘yan ta’adda
Kaduna - Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya hana da fasinjoji 23 na jirgin kasa da suka samu ‘yanci a ranar Laraba a asibitin makarantar horar da hafsoshin soji dake Kaduna.
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da hakan a wata wallafa da tayi a Twitter a ranar Alhamis.
An sako sauran fasinjojin 23 da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar Laraba.
Kamar yadda takardar Garba ashe hi tace, Buhari yayi ziyarar ba-zata zuwa asibitin domin ganin fasinjojin da suka samu ‘yanci.
Ya fara da kaddamar da aji na 69 na sojojin sama, kasa da ruwa na NDA dake Afaka.
Kafin hawa jirgin sojin Najeriya zuwa Abuja, Buhari ya ziyarci asibitin inda ya yabawa sojojin kan gwarzantakarsu ta yadda suka ceto fasinjojin cikin kwanciyar hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojinmu Gwaraza ne, Babu Aikin da Ba Zasu Iya ba: Buhari Yana Murnar Dawowar Fasinjojin Jirgin Kasa
Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya bayyana farin cikinsa kan sakin fasinjoji 23 na jirgin kasa da suka dade a hannun ‘yan ta’adda.
Buhari ya sanar da hakan a ranar Laraba ta wallafar da yayi a shafukansa na soshiyal midiya, jaridar TheCable ta rahoto.
A ranar Laraba aka rahoto yadda fasinjoji 23 na farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suka shaki iskar ‘yanci.
Wannan ‘yancin ya biyo bayan watanni shida da suka kwashe a hannun ‘yan ta’adda.
Asali: Legit.ng