An Kama Matar Da Ta Kashe Yar Aikinta Da Duka Ta Jefar Da Gawar A Daji

An Kama Matar Da Ta Kashe Yar Aikinta Da Duka Ta Jefar Da Gawar A Daji

  • Jami'an hukumar yaki da fataucin mutane da laifuka masu alaka, NAPTIP, sun kama wata mata a Jihar Anambra kan kisar yar aikinta
  • Matar, wacce ba a bayyana sunanta ba ta magantu kan yadda ta yi wa yar aikinta duka, ta fara shure-shure kuma a garzaya da ita asibiti amma ta cika
  • Wacce ake zargin ta ce bayan yar aikin ta rasu ne sai ta yanke shawarar ta tafi wani daji ta jefar da gawarta ta yi tafiyar ta gida

Jihar Anambra - Hukumar da ke hanna fataucin mutane a Najeriya, NAPTIP reshen Jihar Anambra ta kama wata mata da ba a riga an bayyana sunanta ba kan kashe yar aikinta, The Punch ta rahoto.

Taswirar Anambra.
An Kama Matar Da Ta Kashe Yar Aikinta Da Duka Ta Jefar Da Gawar A Daji. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

A wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta, a ranar Alhamis, wacce ake zargin ta kai jami'an Hukumar NAPTIP zuwa dajin da ta jefar da gawar yar aikin na ta.

Kara karanta wannan

Son gaskiya: Soyayya ta sa wata kyakkyawar mata ta auri makaho, bidiyonsu ya ba da mamaki

Bayanai sun nuna cewa wacce ake zargin ta yi wa yar aikin duka, sannan ta fara shure-shure kuma ta rasu kafin a kai ga asibiti.

Wacce ake zargin sai ta dauki gawar yar aikin nata ta jefar a cikin daji.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Na jefar da gawarta a daji bayan ta rasu - wacce ake zargi

A cikin bidiyon da ke yawo a shafukan intanet, wacce ake zargin ta ce:

"Na yi mata duka sai ta fara shure-shure don haka sai na kai ta asibitin Kings Hospital. Bayan mun isa wurin, ta mutu, sai na jefar da gawar ta a nan."

Mahukunta sun bayyana cewa ana cigaba da zurfafa bincike a kan lamarin.

Katsina: An Kama Matar Aure Yar Shekara 20 Kan Kashe Yar Kishiyarta Jinjira Yar Wata Bakwai

A wani rahoton, Kotu ta bada umurnin a tsare mata wata matar aure, yar shekara 20, Lamratu Nasiru, a gidan gyaran hali kan kashe yar kishiyarta, jaridar The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ummita: Kotu ta Dage Sauraron Shari'ar 'Dan Chana da Ya Halaka Budurwarsa Saboda Rashin Tafinta

An rahoto cewa Lamratu ta doki jinjira yar wata bakwai ne a kai da sanda yayin da suke rikici da mahaifiyarta, Zabbau Nasiru.

Lamratu da Zabbau matan wani Malam Nasiru ne a wani Kauyen Unguwar Shalele da ke karamar hukumar Matazu na jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel