Jika Wahal Da Kaka: Sabbin Hounan Tinubu Yana Wasa Da Kyawawan Jikokinsa Sun Bayyana
- Sabbin hotunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, tare da jikokinsa sun bayyana
- Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad ya bayyana Tinubu a matsayin mutum mai matukar son ahlinsa
- Hotunan da ya yadu a shafukan soshiyal midiya a ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoba, ya haddasa cece-kuce daga yan Najeriya
Sabbin hotunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yana shakatawa da jikokinsa sun bayyana a shafukan soshiyal midiya.
Hotunan wanda hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmed, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoba, sun haifa da martani daga yan Najeriya.
Ahmed ya rubuta a kasan hotunan:
“Barka da safiya daga dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, da jikokinsa. Mutum mai son iyali."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, Ahmad bai bayyana a inda aka dauki hotunan ba domin dai tsohon gwamnan na jihar Lagas yana a kasar Ingila yanzu haka.
Jama'a sun yi martani
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:
Kekere Youths ya yi martani:
"Shugaban kasa na gaba da izinin Allah."
Fatima Kaita ta ce:
"Shi jikan namijin kunnuwan shi iri daya da kakan sai dai yafi kakan haske. Hala uwa su baturiya ce BAT 2023."
Isah Lukman Azare ya ce:
"Wai Shi Ba Zai Iya Tsayawa Shi Kadai Ba Ne, Dole Sai Ya Jingina A Jikin Wani Ko Wasu? ."
Malam Abuy Abba Akhuwa ya ce:
"Haka kuka mana da Bahari."
Ishaq Muhammad Iliyasu ya ce:
"Allah mai iko fari a cikin baki ."
Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja
A wani labarin, mun ji cewa ana sanya ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai dawo kasar a ranar Juma’a ko kafin ranar, jaridar TheCable ta rahoto.
Dan takarar jam’iyyar mai mulki ya shafe tsawon wasu yan kwanaki baya a kasar nan. Lamarin ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya inda ake ta cigiyar ina Tinubu ya shiga.
Hakan ya samo asali ne bayan rashin ganin tsohon gwamnan na jihar Lagas a wajen kulla yarjejeniyar zaman lafiya gabannin babban zaben na 2023.
Asali: Legit.ng