Bayan shekaru 3, 'Yan sanda Sun Mika Gawawwakin Wasu 'Yan Shi'a

Bayan shekaru 3, 'Yan sanda Sun Mika Gawawwakin Wasu 'Yan Shi'a

  • Hukumar 'Yan sanda sun mika gawawwakin mabiya darikar Shi'a bayan shekaru uku da mutuwarsu
  • A ta bakin mai magana game da wannan nasara da darikar ta, ta tabbatar da cewa akwai karin wasu gawawwakin da rundunar ta sandan ke rike da su
  • Sun kuma sha alwashin daukar wani mataki game da sauran gawawwakin da ke hannun yan sandan

Hukumar ƴan sanda ta miƙa gawawwakin mabiya ɗarikar Shi'a waɗanda ake zargin ƴan sanda sun kashe su ne a shekarar 2019 a yayin wata zanga-zangar neman sakin shugabansu Alzakzaky da suka yi.

A wani jawabi da ta fitar, Halima Aliyu, a madadin ɗarikar ta shi'a, ta bayyana cewa akwai ƙarin gawawwaki shida a hannun rundunar ta ƴan sanda, kuma sun sha alwashin bin hanya ta Shari'a domin karɓo su, rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Jami’an Kwastom Sun Kama Bindigu, Harsasai, Buhun Shinkafa 7000 Da Jarkokin Mai

Shi'a
Bayan shekaru 3, 'Yan sanda Sun Mika Gawawwakin Wasu 'Yan Shi'a
Asali: Depositphotos

Jawabin nata dai shi ne:

"Za mu so sanar da al'umma cewa ƴan sanda dai sun fara sakar mana gawawwakin mabiya wannan ɗarika tamu da suka yi zanga-zangar neman a saki Sheik Zakzakky."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A sakamakon martani da muka mayar a taron manema labarai da muka yi a ranar 3 ga watan Oktoba, 2022 na Allah-wadai da shugaban ƴan sanda tare da cigaba da neman haƙƙinmu, wanann ta sa an sakar mana gawawwakin mutum 3 cikin 9 da ke hannun rundunar tun bayan zanga-zangar neman a saki shugabanmu"
“An dai kashe mana magoya baya ne a ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, 2019 a babbar sakatariya ta ƙasa a yayin nuna rashin jin daɗinmu wajen tsare shugabanmu ba bisa ƙa'ida da matarsa, Zeenah Ibrahim Alzakzaky."
"Yan sandan sun dai buɗe wuta ne a kan masu zanga-zangar wanda ya jawo kashe mutane 12 da ke yin zanga-zangar, da wani mataimakin Kwamishinan ƴan sanda, Usman Umar da kuma ɗan jarida haziƙi, Owolabi (ma'aikacin Channels TV)."

Kara karanta wannan

Kaduna 2023: Uba Sani da Wasu Yan Takara 16 Sun Shiga Jerin Sunayen INEC Na Karshe

Ta kara da cewa bayan wannan zanga-zanga ne, ƴan sandan suka kwashe gawawwakin waɗanda aka kashe, inda aka watsar da mutane 4 a babban asibitin ƙasa da ke Asokoro.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel