Bidiyon Yaro Makanike Na Zuba Turanci Ya Ba Jama’a Mamaki

Bidiyon Yaro Makanike Na Zuba Turanci Ya Ba Jama’a Mamaki

  • Wani yaro dan Najeriya mai suna Mubarak ya siye zukatan jama'a a TikTok yayin da aka ga bidiyonsa yana zabga turanci
  • A gajeren bidiyon da aka yada, an ga Mubarak sanye da yagaggun tufafin aikin kanikanci yana tafka muhawara kan wani maudu'i
  • Kalaman Mubarak sun ba 'yan TikTok mamaki, sun shiga mamamkin dalilin da yasa yaron baya zuwa makaranta

Dandazon mutane a shafin TikTok sun kamu da kaunar wani yaro mai suna Mubarak saboda irin kwazon da yake dashi.

Hakan ya fara ne daga wani bidiyon da @ayofeliberato ya yada na lokacin da Mubarak ke karanta wata muhawara da ta dauki hankali ya yadu a intanet.

Kwarewarsa a yaren turanci ta ba jama'a mamaki, wannan yasa suka ce ya yi matukar burge su.

Mustapha, makanike dake zuba turanci
Bidiyon Yaro Makanike Na Zuba Turanci Ya Ba Jama’a Mamaki | Hoto: TikTok/@ayofeliberato
Asali: UGC

Mubarak, wanda yaro ne a shagon masu sana'ar kanikanci yana muhara ne kan yin karatu da rana a madadin dare.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi karin haske kan bidiyonsa da aka gani yana umartar sojoji su zane ma'aikata a jiharsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kawo hujjojinsa masu daukar hankali, inda ya ce dare mahutar bawa ce, don haka babu batun karatu da dare, sai dai da rana.

Kalli bidiyon:

Me yasa Mubarak ba ya zuwa makaranta?

Bayan ganin bidiyon, da yawan jama'a a TikTok sun shiga mamakin dalilin da yasa yaro mai kwazo kamar Mubarak ba a ganshi a makaranta ba.

Sun bayyana bukatar dalilin da yasa yaron ke zuwa wurin gyare-gyaren injuna a madadin makaranta don karatu.

Ba a dai tabbatar ba ko yaron ba ya zuwa makaranta kwata-kwata, ko kuma yana aikin kanikanci ne a lokutan hutu ko karshen mako.

Ga dai kadan daga abin da mutane ke cewa:

@bhadboi Nel$ yace:

"Irin wadannan ne yaran da peter obi zai tallafawa."

@fortunecedric yace:

"Don Allah ya kamata wannan bidiyon ya yadu sosai."

@Elubod yace:

Kara karanta wannan

Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

"Me yasa yake koyon sana'ar kanikanci."

@user1200126718789 yace:

"Allah ya yi maka albarka yaro. Ina matukar alfahari da kai saboda wannan."

@user1923428674135 yace:

"Allah ya yiwa duk hazikai a Najeriya albarka.

@Sammy Osaretinmwen Uwaifo yace:

"Wannan wani babban haziki za a yi a nan gaba."

@Yvonne yace:

"Wayyo, yana bata basirarsa a nan. Allah ya turo mai taimakonsa."

@Kazeem Adigun yace:

"Abin mamaki. A ina wannan yaron yake?"

@dotuna3 yace:

"Ya kamata wannan yaron ya ci gaba da karatu don Allah."

@attehdaniel yace:

"Ya kamata ya samu tallafin karatu."

Dalibar Jami’a a Najeriya Ta Samu Karuwa, Ta Haifi ’Ya’ya Biyar a Lokaci Daya

A wani labarin, Oluomachi Nwoye, dalibar ajin karshe a jami'ar ilimin noma ta Michael Okpara ta samu karuwar jarirai biyar a rana daya a asibitin tarayya na Umuahia a jihar Abia.

Mahaifiyar Oluomachi ta ce jariran biyar da diyarta ta haifa sun hada da maza biyu da mata uku, kuma ta haihu ne da misalin karfe 9:15 na dare.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

A wani rahoton Vanguard, an ce biyu daga jariran kuma maza na karbar kulawa ta musamman kasancewar an haife su da 'yar matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.