Shugaba Buhari Ya Yi Nadi Mai Muhimmanci A Ma'aikatar Pantami

Shugaba Buhari Ya Yi Nadi Mai Muhimmanci A Ma'aikatar Pantami

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Adepoju Adeyemi a matsayin sabon babban shugaban aiki na NIPOST
  • A cewar sanarwa da ma'aikatar sadarwa da tattalin arziki ta fitar, anyi nadin ni bisa shawarar Isa Pantami, ministan ma'aikatar
  • Sanarwar ta ce nadin da aka yi wa tsohon dan majalisar wakilan na wa'adin farko na shekaru biyar zai fara aiki nan take

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabon babban shugaban aika, PMG, na Hukumar Aika Saƙonni ta Najeriya (NIPOST).

The Nation ta rahoto cewa wanda aka nada shine Hon Adepoju Adeyemi Sunday, tsohon mamba na majalisar wakilai na tarayyar Najeriya.

Buhari Signs
Shugaba Buhari Ya Yi Nadi Mai Muhimmanci A Ma'aikatar Pantami. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Farfesa Pantami ya tura wa Shugaba Buhari sunan Adepoju

Nadinsa, a cewar kakakin ma'aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani, Uwa Suleiman, ya biyo bayan amincewa ne daga Farfesa Isa Ali Pantami.

Kara karanta wannan

Fitaccen Malamain Musulunci a Arewa Ya Rasu Sakamakon Ambaliyar Ruwa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar da Uwa ta fitar ya ce sabon PMG din na Hukumar NIPOST an nada shi ne na wa'adin farko na shekaru biyar.

Uwa Suleiman ta ce:

"Hon Adepoju kwararren akanta ne kuma tsohon dan majalisar wakilai na tarayyar Najeriya daga 2011 - 2015 kuma daga 2015 - 2019, ya wakilici mazabar Ibarapa East/Ido.
"NIPOST hukuma ce karkashin ma'aikatar Sadarwa da tattalin arzikin zamani kuma nadin da aka yi wa Hon. Adepoju a matsayin shugaban PMG na NIPOST zai fara aiki ne nan take."

Buhari Ya Nada Kwarrren Dan Jarida Matsayin Sabon Shugaban NTA Na Kasa

A wani rahoton, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada Mr Salihu Dembos a matsayin direkta-janar/babban shugaba na Gida Talabijin Na Najeriya, NTA.

Ministan Sadarwa da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, The Punch ta rahoto.

Ya ce nadin da aka masa na tsawon shekaru uku ne a karon farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164