Kano: Hotunan Yadda Daliban Cibiyar Koyar Da Sana'o'i Suka Yi Zanga-Zanga Kan Korarsu Daga Makaranta

Kano: Hotunan Yadda Daliban Cibiyar Koyar Da Sana'o'i Suka Yi Zanga-Zanga Kan Korarsu Daga Makaranta

  • Wasu daliban cibiyar koyar da sana'o'i ta Dangote mallakar gwamnatin jihar Kano sun yi zanga-zanga kan korarsu
  • Wadanda suka yi zanga-zangar sun yi tattaki zuwa harabar majalisar dokokin jihar Kano suna kira ga majalisar da gwamnati ta saka baki a mayar da su
  • Daliban ta bakin jagoransu Abubakar ya ce sabon shugaban cibiyar Paul Quinn ne ya kore su don yana son ya rage kudin kashewa

Jihar Kano - Wasu dalibai na Cibiyar Koyar Sana'o'i ta Dangote, mallakar gwamnatin Jihar Kano, a ranar Talata sun yi zanga-zangar korarsu daga makarantar.

Daliban da aka kora, da adadinsu ya kai dari uku sun yi dandazo a Harabar Majalisar Dokoki ta Jihar Kano a ranar Talata suna bukatar yan majalisaar da gwamnatin jihar ta saka baki a batun.

Kara karanta wannan

Ba a warware yajin ASUU ba, Buhari zai fara ba daliban jami'a tallafi a duk zangon karatu

Kano Sch
Hotunan Dalibai Da Suka Yi Zanga-Zanga Kan Korarsu Daga Makarantar Koyar Da Sana'o'i A Kano. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

Daliban da Abubakar Isma'il ya yi wa jagoranci, ya yi ikirarin cewa an kori kimanin dalibai 400 zuwa 600 ba da 'hakki ba'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daliban sun fadi dalilin korarsu

Da aka musu tambaya, daliban sun yi ikirarin cewa sabon shugaban makarantar, Paul Quinn, dan kasar Indiya, ne ko son ya rage kudaden da aka kashewa a cibiyar.

Amma, wasu majiyoyi sun shaida wa Premium Times cewa an kori daliban ne domin da dama cikinsu ba su cika zuwa aji ba sai jefi-jefi.

Mr Ismail ya ce:

"Muna rokon gwamnati ta taimaka ta shiga tsakani domin a mayar da mu cibiyar mu kammala horaswar kuma mu samu abubuwan da aka mana alkawari, in ji jagoran masu zanga-zangar."

Wasu daliban suna dauke da takardu masu rubutu da ke neman a cire shugaban cibiyar, Paul Quinn.

An yi kokari yin magana da mahukunta cibiyar amma ba a yi nasara ba.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku

Lokacin da Premium Times ta ziyarci cibiyar da ke 'Kwanar Gurjiya' a birnin na Kano, Mr Quinn ya ki yin magana da manema labarai kan lamarin.

Kano Sch
Hotunan Dalibai Da Suka Yi Zanga-Zanga Kan Korarsu Daga Makarantar Koyar Da Sana'o'i A Kano. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

Kano Sch
Hotunan Dalibai Da Suka Yi Zanga-Zanga Kan Korarsu Daga Makarantar Koyar Da Sana'o'i A Kano. @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel