NDLEA ta Cafke Tsohon ‘Dan Kwallo ya Shigo da Kwayoyi daga Kasar Waje a Jirgi

NDLEA ta Cafke Tsohon ‘Dan Kwallo ya Shigo da Kwayoyi daga Kasar Waje a Jirgi

  • Hukumar nan ta NDLEA tana cigaba da kokari wajen yakar masu sha da fataucin kwayoyi a Najeriya
  • A wata sanarwa da ta fito daga bakin Femi Babafemi, an ji yadda aka kama wani tauraro da hodar iblis
  • Emmanuel Okafor ya biyo jirgin Ethiopian Airlines dauke da miyagun kwayoyi daga kasar Brazil

Abuja - Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta cafke wani tsohon ‘dan wasan kwallo da zargin shigo da kwaya.

Sanarwar da ta fito daga Femi Babafemi a ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba 2022, tace an kama tsohon ‘dan wasan ne a filin jirgi na MMIA da ke Legas.

Mista Femi Babafemi wanda shi ne Darektan yada labarai da wayar da kan jama’a na NDLEA yace ana zargin Emmanuel Okafor da shigo da hodar iblis.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hukumar 'yan sanda ta kori wasu manyan jami'anta 7, ta ragewa 10 girma

Emmanuel Okafor ya shigo jirgin saman Ethiopian Airlines daga birnin Sao Paulo a kasar Brazil, ya biyo ta birnin Addis Ababa kafinsu ya sauka a Ikeja.

Da aka sauka a filin sauka da tashin jirgin sama na Murtala Muhammad a Legas ne aka samu wannan ‘dan shekara 33 dauke da kilo 1.4 na hodar iblis.

Magana ta fara fitowa

Jawabin NDLEA yace hirar da aka yi da Emmanuel Okafor yayin da aka soma bincike ya nuna ya bugawa kungiyar UTH Enugu FC kwallon kafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NDLEA
Kamen da NDLEA tayi Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

A shekarar 2014 ‘dan wasan ya bar kungiyar ya koma kasar Sri Lanka, ya yi shekaru biyu a can.

Daga Sri Lanka ne matashin ya samu damar tafiya kasar Brazil domin cigaba da tamula, amma bai cin ma burinsa ba saboda bai da takardun ketare.

Chinedu Ibeh ya fada hannu

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Jaridar Premium Times tace binciken da aka yi ya kuma nuna wani mai dawowa daga kasar ta Brazil, Chinedu Ibeh ya yi yunkurin shigowa da kwayoyi.

Ibeh mutumin garin Ahiazu ne a karamar hukumar Mbaise a Imo. Shi kuma ana tuhumarsa da kokarin shigo da kilogram 3.2 na kwayar da ke kira “Lucci’’

Kamar yadda Sahara Reporters ta kawo rahoto, an biya wannan mutumi N3.1m domin ya shigo da kwayar Najeriya, amma bai yi nasarar lashe kudi ba.

An sace motar Liman ana sallah

Kun ji labari cewa a lokacin da Musulmai suke sallar Juma’a a makon jiya, sai wasu barayi suka sace motar limamin, ko da aka fitomasallaci, ba a ganta ba.

Bayan kwana biyu sai aka ji sanarwa daga Kakakin Rundunar 'Yan Sandan reshen Jihar Kano yana cewa an kama barayin motar malami a garin Zariya.

Kara karanta wannan

Pantami Ya Jagoranci Najeriya da Afrika Sun Samu Gagarumar Nasara a Duniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel