Hukumar ’Yan Sanda Ta Kori Manyan Jami’ai 7, Ta Ragewa 10 Matsayi

Hukumar ’Yan Sanda Ta Kori Manyan Jami’ai 7, Ta Ragewa 10 Matsayi

  • Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta dakatar da wasu jami'anta bisa zarginsu da aikata ayyukan rashin da'a
  • Hukumar ta warware matsaloli 47 a zaman da take a kwanan nan don ganin an duba lamurran ladabtarwa
  • Ana yawan samun korafe-korafe game da yadda 'yan sandan Najeriya ke aiki, lamarin da ke kara jan hankalin jama'a

FCT, Abuja - Hukumar aikin dan sanda ta PSC ta sanar da korar wasu jami'ai bakwai saboda halin rashin da'a a ranar Talata 4 ga watan Oktoba.

Haka nan, hukumar ta kuma amince da rage girman wasu manyan jami'ai 10 nata, inji rahoton Daily Trust.

Wannan mataki na zuwa ne a ci gaba da zama na 15 na hukunci da da sauraran koke da hukumar ke yi a kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Hukumar 'yan sanda ta kori manyan jami'anta saboda rashin da'a
Hukumar 'yan sanda ta kori manyan jami’an ‘yan sanda 7, ta rage wa 10 matsayi | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An ruwaito cewa, zaman da hukumar ke yi zai kare ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Okotoban wannan shekarar, haka nan shafin yanar gizo na LindaIkeji ya tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaman, wanda mukaddashin shugaban hukumar, Justice Clara Ogunbiyi ke jagoranta ya duba duk wasu batutuwan da suka shafi ladabtarwa da ke gaban hukumar.

An warware matsalolin ladabrtawa 47 tare da sauraran daukaka kara daga wasu korarrun jami'ai.

Jami'an da aka kora

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman a Abuja, kakakin PSC, Ikechukwu Ani ya ce manyan jami'an da aka kora sun hada da; CPS daya, SP daya, da ASP biyar.

Hakazalika, ya kuma ce, akwai SP daya ya yi murabus saboda tsira da mutuncinsa. Kana, hukumar ta ragewa CSP daya girma zuwa SP, SP uku zuwa DSP, da kuma DSP biyu zuwa ASP.

Kara karanta wannan

Buhari Zai Karrama Sarkin Kano, Sarkin Zazzau Da Wasu Sarakuna 18 Da Lambar Girma Ta Kasa

Haka nan, an ragewa wasu ASP hudu girma zuwa sufetoci.

Hakazalika, an hukunta wasu jami'an da dama bisa laifuka daban-daban da suka aikata.

A bangare guda, ya shawarci jami'an 'yan sanda da su yi aiki tare da bin doka da oda kamar yadda tsarin aikin dan sanda ya tanada.

An Kama Shugaban Autonation Motors, Nsofor Chukwukadibia da Laifin Mallakar Kwayoyin Tramadol

A wani labarin, an kama biloniya kuma shugaban kamfanin Autonation Motors Ugochukwu Nsofor Chukwukadibia bisa gano ya mallaki kwayoyin Tramadol miliyan 13.4 a wani katafaren gini da ke Victoria Garden City a jihar Legas.

Hukumar NDLEA ta sanar da wannan lamari ne a ranar Lirinin 3 ga watan Oktoba a Lekki ta jihar Legas, PM News ta ruwaito.

A cewar mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafeni, an kama kayayyakin Tramadol da suka kai darajar akalla N8.86bn a ginin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.