Bayan Cika Baki Zai Iya Shan Kwalba 11, Magidanci Ya Sheka Barzahu Bayan Shan Kwalba 9 Na Burkutu A Plateau

Bayan Cika Baki Zai Iya Shan Kwalba 11, Magidanci Ya Sheka Barzahu Bayan Shan Kwalba 9 Na Burkutu A Plateau

  • Wani magidanci a karamar hukumar Bokkos ta Jihar Plateau ya rasu bayan shan kwalaben burkutu guda 9 a Plateau
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutumin da ba a bayyana sunansa ba ya cika baki cewa zai iya shan kwalba 11 ba tare da ya bugu ba
  • Amma bayan ya kwankwadi kwalabe tara cikin 11, ya gaza shanye sauran kuma ya fadi nan take yana fitar da jini daga baki da hanci da kunne

Plateau - Wani mutum da ba a riga an gano sunansa ba a karamar hukumar Bokkos ta Jihar Plateau, wanda ya yi barazanar zai iya shan kwalabe tara na giyar gargazajiya (burkutu) ta tare da ya bugu ba ya mutu.

Hafsat Abubakar ta cibiyar shugabannin mata da sulhu ta Women Leaders of the Conflict Mediation Mitigation Regional Council (CMMRC) reshen jihar Plateau ta tabbatar da lamarin.

Kara karanta wannan

Nima Ban Tsira Ba: Wani Gwamnan Najeriya Ya Ce Ambaliyar Ruwa Ta Ci Gidansa

Taswirar Plateau
Wani Magidanci Ya Sheka Barzahu Bayan Kwankwadar Kwalaben Burkutu 9 A Plateau. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce mutumin da ba a gano sunansa ba ya bukaci mai sayar da burkutun ta bashi kwalabe 11 ya rantse zai iya shanye wa ba tare da ya bugu ba ko wani kunya ya faru.

Yadda lamarin ya faru

Abubakar, wacce aka bawa labarin abin da ya faru a wurin shan burkutun, ta shaidawa The Nation cewa mutumin ya shanye kwalabe tara amma ya gaza shanye sauran biyun.

Nan take mutumin ya mutu yayin da mai sayar da burkutun ta tattara kayan ta ta tsere.

Kafin mutumin ya rasu, ya rika aman jini ta hancinsa da kunne da baki.

Majiyar ta kara da cewa wani mafarauci, wanda ke wucewa ya ga gawar mutumin, ya sanar da mutanen kauyen su tafi su birne shi.

An ce marigayin yana da matar aure daya da yara biyar.

Kara karanta wannan

Gwamnati ba za ta iya rike jami'o'i ba, ya kamata iyaye su fara kawo tallafi, inji gwamnan APC

Abin da wasu likitoci suka ce game da shan biya

Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu likitoci domin sanin menene hatsari ko amfani da ke tattare da shan (Ogogoro) idan akwai.

Dr Nasir, wanda ke aiki a babban asibitin Daura, Jihar Katsina ya ce shi burkutu yana dauke da sinadarin alcohol (giya) mai yawa, kuma yana da hatsari ga lafiyar dan adam, amfanin kalilan ne don haka ya fi kyau a guje masa.

Ya ce:

"Yana kara yiwuwar kamuwa da ciwon hanta (liver cirrhosis) da ciwon daji wato kansa daban-daban.
"Akwai yiwuwar mai shanta ya shaku da abin ya gaza dena sha (addiction) kuma idan an saba sha dole a kara yawan abin da ake sha."

A bangarensa, Dr Jami'u Bello wanda ke aiki a Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Maiduguri ya ce a takaice dai giya na iya kara yiwuwar kamuwa da cutar hanta, cutar Pancreatitis, ciwon kwalkwal (encephalopthy), karuwar kiba, hawan jini da sauransu.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Amince a Raba Buhunan Kayan Abinci 240, 000 a Wuraren da Aka Yi Ambaliya

Dr Jami'u ya ce jikin bil adama tana sarrafa na ta nau'in giyan (ethanol) da ake bukata don sarrafa abinci da wasu abubuwan don haka ya bada shawarar a kaurace mata domin illar da ke tattare da ita ya fi duk wani alfano da za a iya samu.

Hukumar Hisbah ta yi nasarar ƙwace kwallaben giya 1,906 a Jigawa

A wani rahoton, Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa, ta ce ta kwace kwallaben giya guda 1,906 daban-daban a samame daban-daban da ta kai a jihar a shekarar 2021, The Punch ta ruwaito.

Kwamandan Hisbah na Jihar, Ibrahim Dahiru, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, a ranar Talata a Dutse.

Dahiru ya ce hukumar ta kwace kwallaben giyan ne a wuraren shan giya daban-daban da otel a jihar yayin samame.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164