Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

  • Wani matashi dan Najeriya ya yanke jiki ya fadi matacce a daidai lokacin da yake tsaka da buga tamola
  • Mutumin mai shekaru 31 bai samu taimakon gaggawa ba lokacin da abun ya faru domin abokan wasansa sun zata hutawa yake yi har sai da suka ji shirun yayi yawa
  • Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da faruwar al'amarin wanda ya wakana a yankin Lekki

Lagos - Wani matashi mai shekaru 31 ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da yake tsaka da buga kwallo a yankin Lekki na jihar Lagas.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan mummunan al’amarin ya afku ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.

An tattaro cewa matashin wanda ba a tabbatar da sunansa ba yana bin kwallo ne lokacin da ya yanke jiki ya fadi.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Tamola
Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Rahoton ya kuma kawo cewa marigayin bai samu taimakon gaggawa ba domin sauran abokan wasansa sun zata yana kokarin daidaita numfashinsa ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kuma rahoto cewa sauran abokan wasan nasa da suka shafe tsawon mintuna 30 suna jiran ya dawo cikinsu sun je daga shi a gefen filin wasan da ya kwanta kawai sai suka gano cewa sam baya motsi.

Wani dan kwallo, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Ndubisi, ya ce an tabbatar da mutuwarsa ne a wani asibiti da aka kai shi.

Kakakin yan sandan jihar Lagas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da cewar dan kwallon ya yanke jiki ya fadi yayin da yake buga tamola.

Hundeyin ya shawarci jama'a da su daina ketare iyaka sannan su huta a duk lokacin da suka ji gajiya. rahoton Vanguard.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan APC Ya Yi Magana Kan Bidiyon Tinubu Da Ake Yaɗa Wa a Kafafen Sada Zumunta

“Kada ku wuce kima. Idan kun gaji, samu wuri ku huta. Bugu da kari, ku dunga zuwa ganin likita lokaci zuwa lokaci. Kamar yadda masu iya zance kan ce, ‘rai daya ne bashi da na biyu.”

Kana Da Kyau: Budurwa ‘Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Saurayi A Cikin Banki, Ta Karbi Lambar Wayarsa

A wani labari na daban, wata budurwa yar Najeriya da ke yin bidiyoyin barkwanci a TikTok ta je shafin intanet don nuna wani bidiyo wanda a ciki ta tsara wani matashi.

A cikin bidiyon, budurwar ta tunkari wani ma’aikacin banki inda ta bayyana masa cewa lallai shi din yana da kyau. Bayan sun sha hannu da shi, sai ta fada masa cewa tafin hannunsa na da matukar laushi.

Mutumin ya karbi wannan yabo da budurwar tayi masa hannu bibbiyu. Bayan ta bar mutumin, sai budurwar ta nuna dan takardar da mutumin ya rubuta masa lambarta a ciki.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku yayi alkwarin marawa Wike baya a shekarar 2027

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng