Shugaba Muhammadu Buhari Ya yi Sabon Nadin Mukami a Gwamnatin Tarayya

Shugaba Muhammadu Buhari Ya yi Sabon Nadin Mukami a Gwamnatin Tarayya

  • Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabon Shugaban da zai jagoranci ragamar NSIA a Najeriya
  • Gwamnatin Tarayya ta nada Mr. Aminu Umar-Sadiq a matsayin sabon Shugaban wannan hukumar
  • Ministar kudi, Zainab Ahmed ta bada sanarwar nadin wasu manyan darektoci biyu da za su rike NSIA

FCT, Abuja - Mai girma Muhammadu Buhari ya amince da nadin Aminu Umar-Sadiq a matsayin sabon shugaban hukumar nan ta NSIA ta kasa.

Wani rahoto da The Cable ta fitar a ranar Litinin ya tabbatar da cewa Aminu Umar-Sadiq zai karbi ragamar hukumar daga hannun Mista Uche Orji.

Wa’adin Uche Orji ya cika a karshen Satumban 2022 domin ya rike wannan mukami a hukumar NSIA sau biyu daga Oktoban 2012 zuwa yanzu.

Baya ga haka, gwamnatin tarayya ta amince da nadin Kolawole Owodunni da Bisi Makoju a matsayin manyan darektoci a wannan hukumar.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Ma'aikatar kudi ta fitar da sanarwa

Rahoton ya nuna Mai taimakawa Ministar harkar kudi wajen yada labarai, Yunusa Tanko Abdullahi ya fitar da jawabi ya bada sanarwar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dokar NSIA ta 2011, shugaban kasa ne yake da hurumin da zai nada wadanda za su rike Darektoci a hukumar bisa shawarar Ministar kudin kasa.

Ministar kudi
Ministar kudi tare da Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: UGC

Hukumar tana aikin kula da wani rukuni na Baitul-mali da ake amfani da shi wurin gina kasa. Darektocin su na da kwarewa a wajen wannan aiki.

Wanene Aminu Umar-Sadiq?

Jaridar Leadership a rahoton da ta fitar a yammacin Litinin, tace Mista Aminu Umar-Sadiq yanzu haka Darekta ne kafin ya zama sabon CEO a NSIA.

Umar-Sadiq shi ne babban Darektan da yake jagorantar sashen gina ayyukan more rayuka, ya taka rawar gani wajen tsarin bunkasa takin zamani a gida.

Kara karanta wannan

Pantami Ya Jagoranci Najeriya da Afrika Sun Samu Gagarumar Nasara a Duniya

Sabon shugaban ya yi Digirgir har biyu a bangaren kimiyyar Injiniyanci daga jami’ar Oxford (Saint John’s College) da Oxford a United Kingdom (UK).

Har ila yau, ya samu kwarewa da horoswa a karkashin Archbishop Tutu Leadership Fellow (ATLF) da shirin Mandela Washington Fellowship (MWF).

Sanarwar tace Sadiq ya yi aiki a bankin Morgan Stanley Investment Bank da wani kamfani mai suna Denham Capital Management duk a kasar Birtaniya.

Rabon lambobin yabo

A jerin da ya shigo hannunmu, kun ji labari mun fahimci wasu masu taya Muhammadu Buhari aiki a fadar Aso Villa za su samu lambar yabo

Baya ga Marigayi Abba Kyari, Gwamnatin tarayya za ta karrama har wasu ‘yanuwa na jini da surukin mai girma shugaban kasa a wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng