Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola
- Wata matashiya yar Najeriya da ke sana'ar jari bola ta sha ruwan yabo a soshiyal midiya yayin da ta bayyana irin harkar da take yi
- A wani bangare na bidiyonta, an ganota dauke da wani buhu da ke kunshe da kayan jari bola a kanta
- Mutane da dama da suka ya raunukan da ta ji sakamakon wannan aiki sun jinjinawa kokarinta
Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa wani bidiyo da ke kunshe da yadda take gudanar da sana'arta na jari bola a watan Satumba.
Ta bayyana cewa kada mutane su yi mamaki idan ta tara kudin siyan mota kirar Marcedes Benz daga wannan sana’a tata.
Budurwar ta nuna raunukan da ta ji sakamakon tattara kayan jari bola daga wurare daban daban tana sanya su a cikin buhuhuna.
Mutane da dama sun jinjinawa kokarinta yayin da wasu da dama suka ce ba duka mata ne ke da karfin yin irin wannan aikin ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tattara martani fiye da 200 da kuma ‘likes’ sama da 19,000.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:
Teflon_D ya ce:
“Ba duka matane za su iya yin irin wannan sana’ar ba faaaa…kawai dai ina ta karanta martani ina dariya.”
Chiemerie Amah ta ce:
“Na so wannan taken…zai zo ya wuce a rayuwarki da izinin Allah.”
Mini me ta ce:
“Hakarki za ta cimma ruwa da izinin Allah.”
deborahmojisola603 ta ce:
“Kina da kyau da kwazo Allah ya albarkace ki.”
Fasaha Tsantsa: Yadda Wani Dan Najeriya Ya Mayar Da Kwantena Ya Zama Hadadden Ofis, Bidiyon Ya Yadu
Ka Yi Kokari: Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani
A wani labarin, wani dan Najeriya ya wallafa wani hadadden bidiyo a TikTok yana mai nuna yadda ya mayar da kwantena suka zama ofis-ofis.
Ya nuno hadaddun ofis-ofis din a shafin TikTok mai suna @tinspaces kuma nan take ya yadu.
Mabiyansa a dandalin sun kayatu da wannan fasaha tasa da kuma yadda aka mayar da kwantenan yayi kyau.
Asali: Legit.ng