Uwa Uwace: Bidiyon Nakasasshiyar Uwa Tana Bai wa 'Diyarta Abinci da Bakinta ya Taba Zukata

Uwa Uwace: Bidiyon Nakasasshiyar Uwa Tana Bai wa 'Diyarta Abinci da Bakinta ya Taba Zukata

  • Bidiyon wata uwa tana amfani da bakinta wajen ciyar da diyarta abinci ya taba zukatan jama’a da dama a soshiyal midiya
  • Matar nakasasshiya ce don haka bata da hannun rike cokali, hakan yasa take amfani da labbanta
  • Yadda tayi dabaran rike cokalin da kuma baiwa yarinyar abincin ya taba zukata a intanet, mutane sun kuma jinjina mata

Wata kyakkyawar uwa ta ja hankulan mutane da dama a soshiyal midiya bayan tayi amfani da labban bakinta wajen ciyar da karamar diyarta.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafin TikTok, an gano uwar tana diban abinci tare da sakawa karamar diyarta a baki.

Uwa da danta
Bidiyon Nakasasshiyar Uwa Tana Bai wa 'Diyarta Abinci da Bakinta ya Taba Zukata Hoto: TikTok/@miminefanmvanyan2
Asali: UGC

Matar mai suna @miminefanmvanyan2 nakasasshiya ce domin dai bata da hannu, a guntule suke.

Hakan bai hanata sauke hakkinta na uba ba domin dai tana amfani da labbanta wajen rike cokali yayin da take ciyar da diyarta abinci.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekaru 20 Ya Auri Matashiyar Budurwa, Bidiyon Aurensu Ya Haddasa Cece-kuce A Intanet

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda take diban abinci tana kaiwa bakin diyar tata ya taba zukatan mutane da dama.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Yadda matar ke kula da diyar tata ya burge masu amfani da TikTok. Sun je sashin sharhi domin jinjina mata.

@alekakol235 ta ce:

“Allah ya albarkace ki ya kuma tsaya maki.”

@reginamutisya616 ta ce:

“Ina taya dukka iyaye mata na duniya murna.”

@tabbylawrence :

“Allah ya albarkace ki sosai.”

@UkemeObong Peter ya ce:

“Allah ya albarkaci dukkan uwaye nagari.”

Ka Fi Mai Hannu: Matashin Da Bai Da Hannaye Ya Ba Da Mamaki Yayin da Yake Tuka Mota Kamar Kwararren Direba

A wani labarin, wani mutumin kasar Kenya mai suna Sammy Bravo ya burge mutane da dama a soshiyal midiya saboda tarin baiwar da Allah yayi masa.

Abun da yasa labarinsa ya bayar da mamaki shine ganin cewa an haife shi ba tare da hannaye ba, amma kuma yana iya yin abubuwa da dama da masu hannu ke yi.

Kara karanta wannan

Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

An gano Sammy, wanda ke karfafawa mutane gwiwa da zantuka yana ayyuka ba tare da taimakon wani ba ciki harda tuka mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel