Buhari Zai Karrama Sarkin Kano, Sarkin Zazzau Da Wasu Sarakuna 18 Da Lambar Girma Ta Kasa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karrama mutane fiye da 400 da lambar girmamawa ta kasa na 2022
- Daga cikin wadanda za a girmama akwai manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, manyan masu fada aji da sauransu
- Sai dai kuma, sarakuna 20 ne suka kai matakin karshe inda Ooni na Ife, da sarkin Kano ke kan gaba a rukunin
An saki jerin sunayen mutanen da gwamnatin Najeriya za ta karrama da lambar girmamawa ta kasa na wannan shekarar.
Legit.ng ta rahoto cewa mutane 437 ne za su samu lambar yabo daga bangarori daban-daban na rayuwa kama daga yan siyasa, yan kasuwa, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da kuma masu nishadantarwa.
Lambar yabon wannan shekarar ya hada da GCON biyar, CFR 54, CON 67, OFR 64, OON 101, MFR 75, MON 56 da FRM 8.
Shugaba Buhari zai gabatarwa kowani mutum da nasa kason lambar girmamawan a fadar shugaban kasa a ranar Talata, 11 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wannen zauren, Legit.ng ta lissafo wasu daga cikin sarakunan da suka samu shiga sahun wadanda za a karrama a wannan shekarar inda su 20 zasu samu lambar yabo ta CFR.
Ga jerin sunayen sarakunan da aka lissafa za a karrama a kasa:
SUNA | MATSAYI | JIHA | LAMBAR YABO | |
1 | Mai martaba Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II | Ooni na Ife | Osun | CFR |
2 | HM Omo N'Oba N'Edo Uku Akpolokpolo Ewuare | Oba na Benin | Edo | CFR |
3 | Mai martaba, Alhaji Aminu Ado Bayero | Sarkin Kano | Kano | CFR |
4 | Mai martaba Ahmed Nuhu Bamali | Sarkin Zazzau | Kaduna | CFR |
5 | Mai martaba Prof James Ortese Ayatse | Tor Tiv V | Benue | CFR |
6 | Mai martaba Abubakar Shehu Abubakar III | Sarkin Gombe | Gombe | CFR |
7 | Mai martaba Alh. Muhammadu ibn Abali Muhammad Idrissa | Sarkin Fika | Yobe | CFR |
8 | Da. Jacob Gyang Buba | Gbong Gwom Jos | Plateau | CFR |
9 | Mai martaba Justice Sidi Bage Muhammad I (JSC Rtd) | Sarkin Lafia | Nasarawa | CFR |
10 | Mai martaba King Dandeson Douglas JAJA | King Jaja na Opobo | Rivers | CFR |
11 | Mai martaba Oba Gabriel Adejuwon | Onisan na Isan | Ekiti | CFR |
12 | Mai martaba Oba (Dr) Aladetoyinbo Ogunlade Aladelusi, Odundun II | Deji na Akure | Ondo | CFR |
13 | Mai martaba Oba Babatunde Adewale Ajayi | Akarigbo na Remo | Ogun | CFR |
14 | Mai girma Ntenyin (Dr) Solomon Daniel Etuk, JP | Oku Ibom Ibibio | Akwa Ibom | CFR |
15 | Mai martaba Igwe Amb. Lawrence Agubuzu | Igwe na Eziama | Enugu | CFR |
16 | Mai martaba King Alfred Diete-Spiff | Shugaban majalisar sarakunan Bayelsa | Bayelsa | CFR |
17 | Mai martaba Ogiame Atuwatse III | Olu na Warri | Delta | CFR |
18 | Mai martaba Eze (Dr) E. C. Okeke | Shugaban majalisar sarakunan Imo | Imo | CFR |
19 | Mai martaba Eze Joseph Ndubuisi Nwabeke | Shugaban majalisar sarakunan Abia | Abia | CFR |
20 | Mai martaba HRM Eze Charles N. Nkpuma | Ciyaman, Ebonyi | Ebonyi | CFR |
Shugaba Buhari Ya Karrama Buratai Da Babban Lambar Yabo Na Kasa
A gefe guda, mun ji cewa tsohon babban hafsan sojojin kasan Najeriya kuma jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, T.Y. Buratai ya shiga jerin wadanda za su samu lambar yabo ta kasa na 'Commander of the Order of the Federal Republic', (CFR).
Tsohon shugaban sojojin da wasu fitattun yan Najeriya guda 436 ne za a karrama da lambar yabon a wannan shekarar.
Kamar yadda Legit.ng ta gano, Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata 11 ga watan Oktoba zai gabatar da lambar yabon da wadanda aka zaba a gidan gwamnati, Abuja.
Asali: Legit.ng