Mata Ta Maka Miji A Kotu Ta Ce A Raba Aurensu Na Shekara 10 Kan Rashin Haihuwa

Mata Ta Maka Miji A Kotu Ta Ce A Raba Aurensu Na Shekara 10 Kan Rashin Haihuwa

  • Alkalin wata kotun kwastamare da ke zamanta a Abuja ya raba auren shekara 10 tsakanin Blossom Ameh da Simon
  • Ameh ce ta shigar da karar a kotu tana mai cewa ta gaji da zama da Simon saboda rashin haihuwa
  • Simon, a bangarensa shima ya fada wa kotu cewa ya yarda a biya wa matar bukatarta kuma kotun ta raba auren amma ta ce a matar ta mayarwa mijin sadaki

FCT, Abuja - Wata kotun kwastamare da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma'a ta datse igiyar wani aure na shekaru 10 tsakanin Blossom Ameh da mijinta, Simon, kan rashin haihuwa, The Punch ta rahoto.

Alkalin kotun, Doocivir Yawe, ya raba auren saboda bangarori biyun sun yi tarayya cewa ba su sha'awan cigaba da zama tare.

Kara karanta wannan

Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

Gudumar Kotu
Mata Ta Maka Miji A Kotu Ta Ce A Raba Aurensu Na Shekara 10 Kan Rashin Haihuwa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Doocivir ya ce:

"Bayanan da aka bada sun nuna cewa bangarorin biyu sun amince a raba auren kuma wanda aka yi kararsa ya ce kotu ta amsa rokon saki da matarsa ta yi.
"Duba da haka, kotu ba ta da wani zabi sai amincewa da rokon saki da wanda ta shigar da kara ta yi. Don haka an raba auren."

Kotu ta umurci matar da mayarwa mijin N50,000 da ya biya matsayin sadaki

"An kuma umurci wacce ta shigar da karar ta mayar wa wanda ta yi kararsa sadakin da ya biya na N50,000."

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta rahoto cewa Ameh ta maka Simon kara a kotu ne tana neman saki saboda ba ta sha'awan cigaba da auren.

Na gaji, zan koma wurin mutane na, Ameh

Ta ce:

Kara karanta wannan

Cin hanci: PDP ta yi martani, ta fadi dalilin da ya sa ta jika asusun bankin mambobin NWC miliyoyi

"Na gaji da wannan auren. Na yi iya kokari na in ga mun haihu amma ba a samu nasara ba.
"An yi min tiyatan IVF sau biyu kuma ba nasara. Ina son in koma wurin mutane na."

Zamfara: Kotun Musulunci Ta Raba Auren Shekara 23 Tsakanin Wani Mutum Da Jikarsa

A wani rahoron, wata babban kotun shari'a da ke Tsafe, a karamar hukumar Tsafe na Jihar Zamfara a ranar Talata ta raba auren shekaru 23 tsakanin wani mutum Musa Tsafe da jikarsa, Wasila.

Yayin yanke hukuncin, alkalin kotun, Malam Bashir Mahe, ya raba auren bayan ya saurari bangarorin biyu wato masu kare da wadanda aka yi kara.

Mahe ya ce auren tsakanin Tsafe da Wasila bai hallarta ba a koyarwar addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164