Nigeria @62: 'Yan Najeriya Sun Gaji Da Shugabannni Gajiyayyu, Peter Obi
- Yawancin Shugabannin Nijeriya sun gaza, dan takaran shugaban kasa na jam'iyyar LP Ya bayyana
- Lokaci babban Zaben 2023, shine lokaci mafi dacewa ga 'yan Nijeriya, su zabi Shugabanni nagari wanda suka dace, a cewarsa
- Najeriya na murnar cika shekaru 62 da samun yancin kai daga wajen turawan mulkin mallaka
Yayin da Najeriya ke cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya ce ‘yan Najeriya da dama sun gaji da salon shugabancin da ake yi tare da kosawa.
Ya kara da cewa "zaben shekarar 2023, wata dama ce da zata bawa ‘yan Nijeriaya sabuwar dama muddin akai abinda ya dace.
A sakonsa na ranar samun ‘yancin kai ga al’ummar Nijeriya, Obi ya ce yana nadamar bayyana cewa a shekaru 62 da samun ‘yancin kai, Najeriya ba ta da wani abu da zata nuna na alfahari.
Sai dai kasar na cigaba da kasancewa tare da fama Cin Hanci da rashawa, Gurbatacciyar gamnati, rashin tsaro, hadi da tabarbarewa tattalin arziki da kuma wulakanta ofisoshin gwamnati.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Obi ya koka kan yadda gwamnati bata wani hubbasa dan ci gaban al’umma, ga kuma talauci da wahalhalu sun yi ‘yan kasa dabaibayi, hadi da sabbin tsananin rayuwa da al’umma ke fuskanta.
Ya ce:
“Bayan safe shekaru 62 da samun ’yancin kai, har yanzu muna fuskantar koma baya a fannin lantarki (har sau bakwai ana samun daukewar wuta, a fadin kasar nan, a shekarar guda); An rufe jami’o’inmu tsawon watanni takwas, Yawan hauhawar farashin kayayyaki more rayuwa.
“Fiye da rabin al’ummar kasar na fama da matsanancin talauci, rashin tsaro da tashe-tashen hankula; kullum ci gaba yake, ga satar man fetur ba tare da wani hukunci ba, ya kuma kara da cewa "ta kowanne bangaren kasar nan jinin al’umma ne zuba ba gyara ba dalili.
“Duk wani koma-baya da al’umma suka shiga yana da alaka da wannan yanayin. Wannan yasa sa al’ummar kasar suka damu tare dasa ran su a zaben 2023 domin ya ba su damar kawo karshen gazawar shugabancin da aka yi a baya da kuma kawo wani sabon salo dan samun sabuwar Nijeriya."
“Lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su tashi dan ganin sun dawo da kasarsu saiti daga gazawar shugabanni, Bangaranci da cin hanci da rashawa da suka dade suna hana ta cigaba.
“Wannan shi ne ‘yancin kai na gaskiya da Najeriya ke bukata. Muna bukatar ‘yancin kai daga ’yan babakere na tattalin arziki, rashin hadin kan a tsakanin kabilu da addinai, da yancin kai daga talauci da ingantaccen ilimi da dai sauransu” .
"Zaben da ke tafe a shekarar 2023 ya kamata ya kasance bisa cancanta, dattaku da mutunta juna domin samu ci gaba mai dorewa a kasar nan."
Obi ya bayyana cewa a shirye yake ya ciyar da al’ummar kasar gaba, idan aka zabe shi, yana mai jaddada cewa,
“Na tsaya tsayin daka wajen ciyar da al’umma gaba, a bangaren samarwa tare da fitar da kayyaki, musamman ta amfani da dabarun zamani.
“Da wannan, za mu iya gina Sabuwar Najeriya muke buri da mafarki. Kuma mu gina al’ummar da kuma ‘ya’yanmu.”
A nasa sakon murnar Samun 'yancin kai, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) na kasa kuma dan takarar kujerar Sanata mai wakiltar Anambra ta tsakiya a jam’iyyar Labour Party, a zaben 2023, Sanata Victor Umeh ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su lura ba tare da la’akari da kabila ko yare ba, ko addini dasu su zabi Peter Obi, don kawo karshen rashin tsaro da matsalolin tattalin arziki a kasar nan.
A cewarsa,
“a wannan lokaci, tarihin kasarnan ya nuna cewa al’ummar kasar ba ta cikin wani yanayi mai kyau, bayan shekaru sittin da biyu da samun ‘yancin kai, ya kamata mu iya tsara kanmu domin ci gaban kasa, amma muna cikin rudani da rashin madafa”
“Zaben 2023 shine lokacin da ya dace ‘yan Najeriya su samu damar zaben shugabanni da kansu. Ya kamata su zabi shugaban kasa nagari a 2023, kuma ina mai sanar da ku cewa “ Peter Obi da abokin takararsa, Yusuf Datti Ahmed sun kasance a matsayin wadanda suka fi dacewa don magance duk kalubalen da 'yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
“Takarar Obi/Datti zata samar wa ‘yan Najeriya tsarin jagoranci nagari wanda zai gyara tare da kawo shugabanci mai tsafta wanda ba’a taba gani ba a shekaru 62 da suka gabata.
Wasu shugabannin sun yi kokari wasu kuma sun gaza. Amma burin mu shine mu dora mutanen da suka dace a kan kujerar mulki. Mu dora Peter Obi a kan shugaban kasa da dukkan ‘yan takarar jam’iyyar Labour da za su mara masa baya.”
Asali: Legit.ng