Babachir Lawal Bai Taba Tsayawa Kiristoci ba Yayin da yake SGF, Limamin Kirista Yayi Tone-tone
- Limamin cocin Living Stone Assembly da ke Jos, Bishop Jonas Katung ya koka akan maganganun da tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal yayi
- Ya bayyana yadda aka tara manyan limaman addinin kirista don tattaunawa da Tinubu don jin hujjarsa ta tsayar da musulmi a matsayin mataimakinsa
- Sai dai a cewarsa, Babachir ya tara duk limaman ya ci fuskarsu, inda ya kira su da limaman bogi wanda hakan yayi matukar fusata kiristocin Najeriya
Jos, Filato: Babban limamin Cocin Living Stone Assembly da ke Jos, Bishop Jonas Katung ya tuhumci tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal da gaza kare hakkin kiristoci da cocin a mulkin Shugaba Buhari.
Katung ya ce tsohon SGF din da yin bari da addininsa inda ya koma more rayuwarsa na tsawon shekaru uku, tunda ya hau kan mulki, The Nation ta rahoto hakan.
Ya yi wadannan zargin ne ta wata takarda wacce ya saki a Jos yayin mayar da martani akan wata takarda Babachir Lawal ya rubuta akansa.
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An janyo hankalin a akan wata takarda da Babachir Lawal, tsohon SGF ta saki inda yayi maganganu marasa dadi akan limanan Pentecostal din da su ka yi taro da Sanata Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC a Abuja ranar 22 ga watan Satumban 2022.”
Ya bayyana cewa an yi zaman ne da dan takarar APC don jin ta bakinsa akan dalilin da yasa ya zabi musulmi a matsayin mataimakinsa maimakon kirista.
“A matsayinmu na limaman coci, kungiyar limaman Pentacostal daga arewacin Najeriya, mun nemi zama da Tinubu, wanda yanzu Haka ake yawan caccaka inda kiristoci da dama ke son bashi dama don ya yi bayani.
“Archbishop John Praise ya janyo masa aya daga cikin bibul, John 7:51 wacce tace kada mutum ya soki wani ba tare da ba shi damar ya kare kansa ba, kuma kudin tsarin mulki ma ya bada wannan dama.
“A taron, manyan shugabanni na kirista ciki har da Archbishop John Praise, wanda shi ne mataimakin Kungiyar Pentacostal ta Najeriya (PFN) da kuma Rabaran Danjuma Byang, duk sun yi magana akan rashin yin adalci ga kiristoci a arewa wanda tsawon lokaci aka dade ana yi, hakan yasa kiristocin Najeriya ke nuna rashin yardarsu akan tsayar da musulmi da musulmi takara da aka yi a APC.”
- Ya kara da bayyanawa.
Bayan gama duk wata shimfida, ya ci gaba da bayyana yadda yayi mamakin yadda Babachir Lawal, ya bude baki ya kira limaman kiristan da aka zauna da su a matsayin limaman karya a takardar da ta saki.
Ya koka akan yadda a mulki Buhari aka yi rashin adalci wurin bai wa kiristoci mukamai wanda Babachir ya rufe bakinsa saboda kare kujerarsa.
2023: An Bayyanawa 'Yan Siyasa Muhimman Wurare 3 da Zasu Kauracewa Yayin Kamfen
A wani labari na daban, wani Lauya masanin tsarin mulki, Kayode Ajulo, ya gargadi ‘yan siyasar Najeriya da jam’iyyun siyasa da su gujewa rashin biyayya ga tanade-tanaden dokar zabe ta 2022, musamman dangane da gudanar da kamfen gabanin babban zabe na 2023.
Ajulo ya tunatar da ‘yan takarar da ke neman mukamai daban-daban a zabe da ke tafe da cewa bisa ga tanadin dokar zabe, an sanya takunkumi da yawa don hana magudin zabe da aka saba farawa ko da lokacin kamfen.
Asali: Legit.ng