Ka Fi Mai Hannu: Matashin Da Bai Da Hannaye Ya Ba Da Mamaki Yayin da Yake Tuka Mota Kamar Kwararren Direba

Ka Fi Mai Hannu: Matashin Da Bai Da Hannaye Ya Ba Da Mamaki Yayin da Yake Tuka Mota Kamar Kwararren Direba

  • Sammy Brayo, mutumin da aka haifa babu hannaye da nakasassun kafafuwa ya baiwa mutane mamaki da yadda yake abubuwansa
  • Abun da yafi bayar da mamaki game da Sammy shine cewa ya iya tuki, iyo a ruwa da kada fiyano duk da halin da yake ciki
  • Wani bidiyo da ya nuno shi yana baje kolin fasaharsa ya yadu a soshiyal midiya kuma ya burge mutane da dama

Wani mutumin kasar Kenya mai suna Sammy Bravo ya burge mutane da dama a soshiyal midiya saboda tarin baiwar da Allah yayi masa.

Abun da yasa labarinsa ya bayar da mamaki shine ganin cewa an haife shi ba tare da hannaye ba, amma kuma yana iya yin abubuwa da dama da masu hannu ke yi.

Kara karanta wannan

Gemu bai hana ilimi: Bidiyon dan shekaru 38 da ya shiga firamare aji uku ya ba da mamaki

Sammy
Ka Fi Mai Hannu: Matashin Da Bai Da Hannaye Ya Ba Da Mamaki Yayin da Yake Tuka Mota Kamar Kwararren Direba Hoto: YouTube/Afrimax English.
Asali: UGC

An gano Sammy, wanda ke karfafawa mutane gwiwa da zantuka yana ayyuka ba tare da taimakon wani ba ciki harda tuka mota.

Matashin ya iya iyo a ruwa sosai yayin da bidiyon ya hasko shi a cikin ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Allah ya yiwa Sammy baiwa iri-iri

Babban baiwar da Allah yayi masa shine ya iya zane sosai, wato bi ma’ana shi kwararren mai zanen hotuna ne.

Ya kuma iya kada fiyano kuma yana da murya mai dadi wanda ke dadada kunnen mai sauraro.

Sammy na burge mutane da dama da suka ga bidiyonsa wanda Afrimax English ya wallafa a YouTube.

Jama'a sun yi martani

Marcelle Spencer ya ce:

“Gaskiya yana da hazaka Allah ya ci gaba da sanya masa albarka.”

Vera Mensah ta ce:

“Yana da matukar kyau da murmushi mai kyau. Shakka babu Allah ya albarkacesa,”

Kara karanta wannan

Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

Belinda Hawkins ta ce:

“Shi din jarumin kansa ne. mutane masu nakasa daban-daban sun karade duniya kuma suna aiki tukuru fiye da yawancin mutane.”

Fasaha Tsantsa: Yadda Wani Dan Najeriya Ya Mayar Da Kwantena Ya Zama Hadadden Ofis, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin, wani dan Najeriya ya wallafa wani hadadden bidiyo a TikTok yana mai nuna yadda ya mayar da kwantena suka zama ofis-ofis.

Ya nuno hadaddun ofis-ofis din a shafin TikTok mai suna @tinspaces kuma nan take ya yadu.

Mabiyansa a dandalin sun kayatu da wannan fasaha tasa da kuma yadda aka mayar da kwantenan yayi kyau. Amma da farko, duk wanda ya kalli kwantenan ba zai taba tunanin cewa zai iya amfani har ya zama ofis ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel