Hukumar Shirya Jarabawa NECO Ta Fitar da Sakamakon SSCE 2022
- Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) ta sanar da sakin sakamakon jarabawar Sakandire ta bana SSCE 2022
- Shugaban hukumar, Farfesa Ɗantani Wushishi, yace sama da kaso 60 na ɗaliban da suka zana jarabawar sun haye
- Haka nan ya bayyana matakin da zasu ɗauka kan waɗanda suka kama da hannu a laifin satar amsa
Niger - Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) ta saki sakamakon jarabawar fita daga Sakandirire SSCE 2022, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Shugaban hukumar, Farfesa Ɗantani Wushishi, shi ne ya sanar da sakin sakamkon a hedkwatar NECO da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
Bayan sakin sakamakon, Wushishi yace hukumar ta ɗiga wa wakilai masu duba jarabawar 29 baƙin fenti bisa kama su da hannu dumu-dumu a aikafa laifukan satar amsa.
Haka zalika yace an shawarci dakatar da makarantu hudu na tsawon shekaru biyu kan aikata laifin satar jarabawa a kai a kai. Yace an samu raguwar sata a 2022 idan aka kwatanta da 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, raguwar samun kes ɗin satar jarabawa abun a yaba ne, inda yace:
"Game da batun satar jarabawa, an kama 13, 595 fiye da 20, 003 da muka kama a 2021, wanda ya nuna cewa an samu ragi sosai da ya cancanci yabo.
Yadda Sakamakon ya kasance
Farfesa Wushishi ya yi bayanin adadin ɗaliban da suka yi rijistar zana jarabawar da, 1, 209, 703 yayin da mutum 1, 198, 412 suka zauna rubuta jarabawar a faɗin Najeriya.
Ya ƙara da cewa alƙaluma sun nuna adadin ɗaliban da suka samu 5 Credit zuwa sama ciki har da darussan Turanci da Lissafi sun kai 727, 864 wato kashi 60.74%.
Bugu da ƙari, Farfesa Wushishi yace adadin mutane masu buƙata ta musamman 1, 031 ne suka zauna jarabawar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A wani labarin kuma Matashi Mai Shekaru 38 Ya Koma Makarantar Firamare Yayin da Matarsa Ta Guje Shi
Wani mutum mai shekaru 38 mai suna John ya kudurta komawa makaranta neman ilimi bayan da matarsa ta yi watsi dashi.
A yanzu dai ya shiga firmare aji uku tare da 'ya'yansa kuma yana fatan kammala karatunsa kana ya zama wani abu a rayuwa.
Asali: Legit.ng