Matashi Mai Shekaru 38 Ya Koma Makarantar Firamare Yayin da Matarsa Ta Guje Shi

Matashi Mai Shekaru 38 Ya Koma Makarantar Firamare Yayin da Matarsa Ta Guje Shi

  • Wani mutum mai shekaru 38 mai suna John ya kudurta komawa makaranta neman ilimi bayan da matarsa ta yi watsi dashi
  • A yanzu dai ya shiga firmare aji uku tare da 'ya'yansa kuma yana fatan kammala karatunsa kana ya zama wani abu a rayuwa
  • John ya ce wannan mataki nasa ya zama dole ne tunda matarsa ta gudu ta barshi, inda ta tare da wani mutum don kawai yana da ilimi

Wani magidanci dan shekara 38 ya bayyana komawa karatu saboda ya nemi ilimin da zai zama wani abu nan gaba.

Matashin mai suna John ya koma makarantar firamare domin ya samu nagartaccen ilimi duk kuwa da yawan shekarunsa.

John dai na da kyakkyawar mata da 'ya'ya biyu, amma da zama ya yi tsami, matar ta guje shi ta bi wani mutum daban, inda ta kira John lusari.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi Ya Ragargaji Gwamnatin APC a gaban Majalisar Dinkin Duniya

Yadda matashi dan shekaru 38 ya koma makarantar firamare
Matashi Mai Shekaru 38 Ya Koma Makarantar Firamare Yayin da Matarsa Ta Guje Shi | Hoto: Afrimax English
Asali: UGC

Wannan abu ya kona masa rai, don haka ya yanke shawarar ya nemi ilimi domin gaba ya zama babban mutum.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An haifi John a gidan talakawa

Matashin ya bayyana cewa, iyayensa talakawa ne, ba su iya daukar nauyin karatunsa a lokacin da yake karami ba.

Saboda haka, John bai san dadin karatu ba sadda yake yaro, kawai ya dukfa da neman kudi wurjajan domin ya iya rike iyalinsa

Biyo bayan rabuwa da matarsa, John ya dumfari makaranta, a ranarsa ta farko, dalibai sun zaci malamin makaranta ne.

Duk da dariyan da ake masa, ya ce shi burinsa ya kammata karatu ne nan da ya cika shekaru 50 a duniya.

Martanin jama'ar intanet

Debbie Fisher yace:

"Ina taya murnar mai da rayuwarka mai kyau. Ina matukar alfahari da kai. Ka ci gaba da aikinka mai kyau.

Kara karanta wannan

Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

Hey_jake yace:

"Irin wannan kokari ba a ko'ina ake samu ba. Lusara dai ita ce matar John kuma ina maka fatan samun wata matar mai tunanin rayuwa irin naka. Matukar za ka iya tashi, to kada ka fidda rai. Wannan ya yi.

Vero Bullock ta rubuta:

"John na da buri mai yawa. Ina kaunarsa"

Barbara Walker tace:

"Haka hangen nesa, tunani da buri yake. Ina karfafa maka gwiwa. Za ka cimma burinka."

Karen Coleman tace:

"Allah ya albarkaci wannan matashin. Yana da matukar ruhin hange nesa wajen tunanin cimma burinsa. Allah ya ba shi nsara har wata rana ya zama malami abin koyi. Zai taimaki mutane da yawa."

Budurwa Ta Ce Watanni 7 Suka Rage Mata a Duniya. Ta Yada Bidiyonta, Ta Koma Ga Allah

A wani labarin, budurwar da ta ce sauranta watanni bakwai ta rayu a duniya ta sa zukatan mutane a TikTok sun cika da jimami da tausayi.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mai Garkuwa da Mutane dake Watsin Daloli a Soshiyal Midiya Yana Zubda Hawaye a Hannun 'Yan Sanda

Budurwar mai suna Malkai ta yada wani bidiyo a TikTok, inda tace ta gaji kuma ba ta da karfin ci gaba da rayuwa.

Ta bayyana cewa, tana matukar kokari don iya rayuwa daidai, amma abubuwan sun ci tura. A kalamanta, cewa ta yi:

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.