Motar Fetur Ta Kama da Wuta, Mutane ‘Fiye da 20’ Sun Babbake Kurmus Nan-take

Motar Fetur Ta Kama da Wuta, Mutane ‘Fiye da 20’ Sun Babbake Kurmus Nan-take

  • Wata mota da ta dauko man fetur ta kife a gada da aka samu wani mummunan hadari
  • Hadarin ya yi sanadiyyar dinbin mutane da-dama, wasu suna cewa akalla mutane 20 sun cika
  • Abin ya auku ne a wata gada da ke garin Ankpa, jami’an FRSC sun tabbatar da lamarin

Kogi - Fiye da mutum 20 ake tunani sun mutu a dalilin wata babbar mota da tayi hadari a kan wata gada a jihar Kogi.

Jaridar nan ta Daily Trust ta kasar nan ta fitar da wannan labari mara dadi a safiyar Alhamis, 29 ga watan Satumba 2022.

Rahoton yace babbar mota ta fadi ne a wa tagada da ke kan ruwan Maboro a karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Wannan mota ta dauka man fetur ne a lokacin da ta fi karfin direbanta, tayi hadari a kan titi.

Abin bai yi kyau ba

Wani wanda abin ya faru a gaban idanunsa, ya shaidawa jaridar cewa motar tayi hadari da kimanin karfe 3:30 na yamma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Babu wanda ya san adadin mutanen da suka mutu yanzu. Mutane suna cikin rafin suna harkokin gabansu, sai motar ta kubce.
Daga nan ta fai, ta tarwatse a kan gadar. Abin babu kyawun gani. Mafi munin abin da na taba gani tun da nake a rayuwata.”

- Inji wani Usman Ahmed wanda mazaunin Ankpa ne.

Motar Fetur
Manyan motoci a hanya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

"Mutane 20 sun rasu"

Wani mazaunin wannan gari ya tsaida adadin gawa a kan mutane fiye da 20, a cewarsa ta kai an gagara gane gawar wasu.

Wannan Bawan Allah yake cewa a cikin jaka aka rika bangaren jikin gawawwaki.

Kara karanta wannan

An kama fasto a jihar Arewa bisa bude asibiti a cocinsa, yana ba da maganin bindiga

"Wannan ne babban masifa na biyu da ya aukawa Ankpa a watan nan. Wannan ya fi muni, fiye da mutum 20 sun mutu.

Wasunsun sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba."

- Inji Mazaunin Ankpa

Rahoton 21st Century Chronicle ya nuna babura sun kone, haka wata mota da abin ya rutsa da ita, ta rasa duka fasinjojinta.

Babban jami’in FRSC na reshen jihar Kogi, Stephen Dawulung yace ba za a iya cewa ga adadin wadanda suka mutu ba tukuna.

Tattakin OBIDATTI a Legas

An ji labari Alkali ya zartar da hukunci a tanar Laraba a kan karar da wasu Lauyoyi suka shigar game da magoya bayan Peter Obi.

Kotu tace za a iya yin tattakin Obidatti23 Forward Ever a Legas a ranar 'yancin-kai, amma da sharadin ba za a taru a kofar Lekki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel