Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra
- Yan bindiga sun farmaki al'ummar yankin Umunze da ke karamar hukumar Orumba ta kudu a jihar Anambra
- Maharan da suka bude wuta sun halaka jami'an sojoji biyar da wani dan farar hula daya
- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da harin amma tace bata samu cikakken bayani kansa ba tukuana
Anambra - Jaridar The Nation ta rahoto cewa tsagerun yan bindiga sun kashe jami’an sojoji guda biyar da wani dan farin hula daya.
An tattaro cewa lamarin ya afku ne a kusa da wani banki a Umunze, yankin karamar hukumar Orumba ta kudu.
Wata majiya da ta zanta da jaridar ta bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 2:00pm na ranar Laraba, 28 ga watan Satumba.
Majiyar ta bayyana cewa sojojin sun kasance a cikin wata motar Sienna ne lokacin da yan bindigar suka farmake su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harbe-harben ya haddasa tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.
Kakakin yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, yace an yi harbe-harbe a kusa da wani banki a Umunze.
Ya ce ba a samu cikakken bayani kan lamarin ba, yana mai cewa abun ya faru ne tsakanin 12 zuwa 12:30 na rana.
Ya kuma bayyana cewa rundunar ta tura jami’an tsaro domin kare yankin, yana mai cewa ya zama dole wadanda suka aikata ta’asar suyi danasani.
Wani babban jami’in dan sanda a jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa shima ya tabbatar da faruwar lamarin ga The Nation.
Sojoji Da Yan Ta'adda Na Musayar Wuta Yanzu Haka A Jihar Arewa
A wani labarin, mun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya na Operation Hadin suna nan suna artabu da mayakan Boko Haram a Maiduguri, jihar Borno.
Jaridar TheCable ta rahoto cewa yan ta’addan sun kaiwa sojojin da ke yiwa motocin kasuwa rakiya kwantan bauna a kauyen Yaleri da ke hanyar Damboa.
A cewar wani jami’in leken asiri wanda ya zanta da Zagazola Makama, wani mawallafi da ya karkata ga yankin Tafkin Chadi, dakarun sun fafata da yan ta’addan yayin da fasinjoji suka bazama neman tudun tsira, rahoton AIT.
Asali: Legit.ng