Yanzu-Yanzu: Sojoji Da Yan Ta'adda Na Musayar Wuta Yanzu Haka A Jihar Arewa

Yanzu-Yanzu: Sojoji Da Yan Ta'adda Na Musayar Wuta Yanzu Haka A Jihar Arewa

  • Dakarun Operation Hadin suna musayar wuta da mayakan Boko Haram a Maiduguri, jihar Borno
  • Yan ta’addan sun kaiwa sojojin da ke yiwa motocin kasuwa rakiya kwantan bauna a kauyen Yaleri da ke hanyar Damboa
  • Matafiya sun rarrabu suna neman wajen tsira yayin da sojojin ke fafatawa da mayakan

Borno - Dakarun rundunar sojojin Najeriya na Operation Hadin suna nan suna artabu da mayakan Boko Haram a Maiduguri, jihar Borno.

Sojoji
Yanzu-Yanzu: Sojoji Da Yan Ta'adda Na Musayar Wuta A Jihar Arewa Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Jaridar TheCable ta rahoto cewa yan ta’addan sun kaiwa sojojin da ke yiwa motocin kasuwa rakiya kwantan bauna a kauyen Yaleri da ke hanyar Damboa.

A cewar wani jami’in leken asiri wanda ya zanta da Zagazola Makama, wani mawallafi da ya karkata ga yankin Tafkin Chadi, dakarun sun fafata da yan ta’addan yayin da fasinjoji suka bazama neman tudun tsira, rahoton AIT.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Machina Ya Kada Ahmad Lawan A Kotu, An Alantasa Matsayin Sahihin Dan Takara

Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutane 7 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jihar Kaduna

A wani labarin, mun ji cewa dakarun rundunar Operation Forest Sanity sun ceto wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a yayin wani fatrol a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun da ke jihar Kaduna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, jaridar The Cable ta rahoto.

Aruwan yace a wani rahoton aiki da suka samu, yan bindigar sun budewa dakarun wuta a yayin da suke aikin fatrol, rahoton PM News.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng