Yan Bindiga Sun Kashe Babban Yaron Dan Majalisa A Jihar Bauchi

Yan Bindiga Sun Kashe Babban Yaron Dan Majalisa A Jihar Bauchi

  • Yan bindiga sun kashe babban dan gidan Bala Ali, dan majalisar dokokin jihar Bauchi bayan kwanaki da saceshi
  • Daukacin majalisar dokokin jihar sun yi alhinin faruwan wannan abu kuma sun gudanar da addu'a
  • Yankin Arewacin Najeriya na cigaba da fuskantar barazanar yan bindiga masu garkuwa da mutane

Bauchi - Babban 'dan Honarabul Bala Ali, Dan majalisa mai wakiltar mazabar Dass a majalisar dokokin jihar Bauchi ya mutu a hannun yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Mai magana da yawun majalisar, Abubakar Suleiman, Abdul Barra, ya bayyana hakan a takardar da ya baiwa manema labarai ranar Talata., rahoton Punch.

Yace dan majalisa mai wakilatar mazabar Burra, Ado Wakili, ya sanar da mutuwar yaron abokin aikinsu a zauren majalisa.

Yan majalisan sun aike sakonnin ta'aziyyarsu ga iyalan Honarabul Bala Ali inda sukayi addu'an Allah ya jikan mamacin.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

Kakakin majalisan ya sanar da cewa zasu kai ziyarar ta'aziyya gidan iyalan mamacin bayan zaman majalisa.

Bauchi
Yan Bindiga Sun Kashe Babban Yaron Dan Majalisa A Jihar Bauchi
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abinda ya faru

Burra yace Baballe Dambam, mai wakiltar Dambam/Zagaya/Jalam ya bayyana yadda yan bindiga suka sace yaron kuma suka rikeshi tsawon kwanaki sannan suka kasheshi.

Yace tuni an gudanar da Sallar Jana'izar.

An Ceto Jaririn Da Wata Mata Ta Sace A Asibitin ATBU Bauchi

A wani labarin kuwa, Hukumomin asibitin koyarwan jami'ar Abubakar Tafawa Balewa ATBUTH dake jihar Bauchi sun bayyana cewa an gano dan tagwayen da aka sace a asibitin makon da ya gabata.

Dr Haruna Liman, Shugaban kwamitin bada shawara na asibitin, yace tuni sun damka jaririn ga mahaifiyarsa a Bauchi ranar Talata, rahoton kamfanin dillancin labarai NAN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel