'Yan Bindiga Sun Kai Hari Wurin Binciken Ababen Hawa Na Sojoji a Enugu
- Rahoto daga jihar Enugu ya nuna cewa wasu mahara sun farmaki shingen binciken ababen hawa na sojoji a Titin Obeagu-Amodu
- Wata majiya tace 'yan sanda da sojoji sun yi kokarin maida martani inda aka yi musayar wuta a yankin na ƙaramar hukumar Enugu ta kudu
- Wannan zuwa ne makonni uku bayan wasu 'yan bindiga sun halaka 'yan sanda uku a New Heaven, jihar Enugu
Enugu - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai hari wurin binciken ababen hawa na dakarun sojin Najeriya dake kan Titin Obeagu-Amodu, ƙaramar hukumar Enugu ta kudu a jihar Enugu.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wannan harin na zuwa ne makonni uku bayan wasu miyagu sun bindige 'yan sanda uku har lahira a yankin New Heaven dake jihar, kudu maso gabashin Najeriya.
Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Da Wasu 3, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawan Gaske A Jihohin Arewa 2
Rahotanni sun nuna cewa yan bindiga sun shiga yankin ne a motocin Lexus RX SUV guda biyu da Toyota Sienna da misalin ƙarfe 7:25 na safiyar yau Talata.
Da isar su yankin a wasu bayanai da aka tattaro, maharan sun buɗe wa haɗakar jami'an 'yan sanda da Sojoji da ke aiki a wurin wuta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Cikin kwarewa da sanin makamar aiki, jami'an tsaro suka maida martani ga maharan, sakamakon haka aka yi wata kazamar musayar wuta a yankin.
Wata majiya ta shaida wa wakilin jaridar Punch cewa harin ya bar mutane da dama cikin mawuyacin hali yayin da wasu suka rasa rayukansu.
Duk da ba'a tabbatar da adadin mutanen da harin ya shafa ba amma wata jita-jita da ake yaɗa wa ta yi ikirarin cewa mutum biyu ne suka rasa rayukansu yayin musayar wuta.
Legit.ng Hausa ta gano cewa lamarin ya jefa tsoro da tashin hankali a zuƙatan mutanen dake rayuwa a yankin da kewaye.
Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda reshen jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe, bai ɗaga kiran waya ko ya amsa sakonnin da ake tura masa domin tabbatar da kai harin ba.
Sojoji sun kashe yan ta'adda a Yobe
A wani labarin kuma Sojoji Sun Harba Manyan Makamai Kan 'Yan Ta'adda, Da Yawa Sun Zarce Lahira
Dakarun sojin Najeriya sun harba makamai masu haɗari kan mayaƙan kungiyar ISWAP bayan samun bayanan sirri a Yobe.
Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa tulin 'yan ta'addan sun rasa rayukansu sakamakon samamen sojin.
Asali: Legit.ng