Kotu Ta Yi Watsi da Bukatun Daliban Jami'o'in Najeriya kan FG da ASUU

Kotu Ta Yi Watsi da Bukatun Daliban Jami'o'in Najeriya kan FG da ASUU

  • Kotun ma'aikata dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta kori ƙarar da ɗalibai suka shigar da ASUU da gwamnatin tarayya
  • Kotun ta ɗauki wannan matakin ne a zamanta na Talata 27 ga watan Satumba, 2022 bayan shugaban tsagin NANS ya bukaci haka
  • Kungiyar ɗalibai ta ƙasa ta shiga rikici tun bayan bayyanar mutum biyu da suka yi ikirarin lashe zaɓen shugaba

Abuja - Kotun ma'aikata (NIC) dake zama a Abuja ta yi fatali da ƙarar da ƙungiyar ɗalibai NANS ta shigar, inda ta nemi a tilasta wa ASUU da gwamnatin tarayya su janye yajin aiki.

Mai shari'a Polycarp Hamman ya dakatar da ci gaba da zama kan shari'ar ranar Talata bayan shugaban tsagin NANS, Umar Faruk Lawal, ya janye ƙarar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kotun ma'aikata ta yanke hukunci.
Kotu Ta Yi Watsi da Bukatun Daliban Jami'o'in Najeriya kan FG da ASUU Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Tribune ta ruwaito cewa Lawal ya shaida wa Kotun cewa shi ne ya shigar da ƙara mai lamba NICN/ABJ/273/2022 a madadin ƙansa da kuma ƙungiyar NANS.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan Na Gab Sanin Makomarsa a 2023

Bayan ASUU da ake tuhuma ta farko a ƙarar, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, sune na biyu da na uku da ake ƙara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da aka dawo don cigaba da zama kan batun yau Talata, Lawal ya sanar da Kotu cewa ya shigar da buƙatar neman dakatar da shari'ar baki ɗaya.

Ya jingina dalilin janyewarsa da kalubalen da ƙungiyar ɗaliban ke fama da shi, wanda ya kai ga hamɓarar da shi daga kujerar shugaban NANS na ƙasa.

Duk da babu wakilan sauran mutum biyu da ake ƙara, Lauyan ƙungiyar malaman jami'o'i, Marshal Abubakar, ya shaida wa Kotun cewa ba ya musu da bukatar Lawal na janye ƙarar.

Daga nan, Alkalin Kotun mai shari'a Hamman bai yi wata-wata ya sanar da yin watsi da ƙarar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan PDP, Gwamna Wike Ya Yi Sabuwar Tafiya

Rikicin shugabanci ya ɓarke a NANS

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa idan baku mance ba 'yan takarar shugabancin NANS biyu suka yi ikirarin lashe zaɓen da ƙungiyar ta gudanar kwanan nan.

Yayin da Lawal wanda ya fito daga jami'ar Bayero University Kano (BUK) ya jaddada cewa shi ne zaɓaɓɓen shugaba, kwamitin shirya zaɓen NANS ya raba gardama tare da ayyana Usman Barambu a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.

A wani labarin kuma kun ji cewa Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

Kotu ta umurci kungiyar malaman jami’a da ta dakatar da yajin aikinta da ke gudana a kasar nan.

Alkalin kotun masana’antu ta kasa, Justis Polycarp Hamman, ya hana ASUU ci gaba da yajin aikin har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan shari’ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel