Wani Matashi Dan Shekara 21 Ya Mutu a Wurin Shagalin Bikin Karin Shekara
- Wani matashi mai suna, Micheal Arigbabuwo, Ya Rasu a wurin bikin karin shekarar Abokinsa a jihar Legas
- Kakakin yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, yace sun kama abokansa uku kuma sun labarta musu abinda ya faru
- Hundeyin ya gargaɗi matasa su guji shan miyagun kwayoyi domin illa ce kaɗai a tattare da halayyar babu wani abun amfani
Lagos - Wani matashi ɗan shekara 21 a duniya, Micheal Arigbabuwo, ya rasa rayuwarsa a wurin shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwa bayan haɗa manyan miyagun kwayoyi da suka sha ƙarfinsa.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, shi ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi.
Mista Hundeyin yace lamarin ya faru ne ranar Jumu'a a yankin Ikorodu, jihar Legas, inda ga ƙara da cewa abokanansa uku waɗanda suka halarci wurin sun shiga hannu.
Kakakin yan sandan yace Jami'ai a yankin Ikorudu sun samu kiran gaggawa da karfe 7:30 na daren ranar Jumu'a cewa wasu tawagar 'yan Yahoo-Yahoo sun kai gawa yankin Igbogbo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hundeyin yace:
"Bisa waɗannan bayanai, tawagar jami'an yan sanda ta ziyarci wurin kuma ta ɗauki hotuna, kana suka kama matasa guda uku, waɗanda shekarunsu basu wuce tsakanin 23 zuwa 24 ba."
"Matasan sun yi iƙirarin cewa suna zargin mamacin ya kwankwadi Codin da wata kwaya a wurin shagalin ƙarin shekara na ɗaya daga abokansu wanda ya gudana a Igbogbo dake Ikorodu."
"Waɗanda ake zargin sun ƙara da cewa nan take Mamacin ya fara shessheƙar nunfashi, an yi gaggawar kai shi Asibiti amma rai ya yi halinsa."
Mai magana da yawun yan sansan yace tuni aka ɗauki gawar zuwa babban Asibitin Ikorodu domin gudanar da bincike.
Yan sanda sun gargaɗi matasa
Bugu da ƙari, SP Hudeyin ya gargaɗi matasa kan wuce gona da irin wajen shan kwayoyi da kuma shan muggan kwayoyi.
"Kuna tunanin shan kwayoyi miyagu? Ku sake tunani domin ba bu wani abu mai kyau da yake fitowa daga halayyar. Mun fara gudanar da bincike kan Kes din."
A wani labarin kuma kun ji cewa An Gano Gawarwakin Mace da Namiji da Suka Mutu Suna Tsaka da Saduwa a Legas
Wasu sabbin bayanai da hukumumi basu faɗa ba sun nuna cewa an zakulo gawar wata mace da namiji tsirara a ginin Legas.
Wasu ma'aikatan agajin gaggawa da suka nemi a sakaya bayanansu sun ce sun mutu ne suna tsaka da jin daɗinsu.
Asali: Legit.ng