An Gano Gawarwakin Mace da Namiji da Suka Mutu Suna Tsaka da Saduwa a Legas
- Wasu sabbin bayanai da hukumumi basu faɗa ba sun nuna cewa an zakulo gawar wata mace da namiji tsirara a ginin Legas
- Wasu ma'aikatan agajin gaggawa da suka nemi a sakaya bayanansu sun ce sun mutu ne suna tsaka da jin daɗinsu
- Hukumomi sun bayyana cewa mutum hudu, maza biyu da mata biyu ne suka rasa rayuwarsu a ginin wanda ya rushe ran Jumu'a
Lagos - Wasu sabbin bayanai da ba'a bayyana ba sun fito game da ruftawar Gini na baya-bayan nan a jihar Legas.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Wani gida a kan layin 2/4 Iye Sonuga, Palm Avenue, ya rushe ranar Jumu'a, inda ya yi ajalin mutum huɗu.
Jami'an ba da agajin gaggawa da suka nemi a sakaya bayanansu sun shaida wa jaridar cewa wasu mutum biyu, Namiji da mace, na tsaka da soyewarsu lokacin da ginin ya rufta.
"A takaice an gano gawarwakinsu tsirara," inji wani ma'aikacin hukumar kwana-kwana da ya nemi a ɓoye sunansa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jami'an da suka yi gaggawar kai agaji daga hukumar kai ɗaukin gaggawa ta ƙasa (SEMA) da ta jihar Legas (LASEMA) da jami'an hukumar kashe gobara sun gama zakulo mutane, hudu sun mutu, an ceto ɗaya.
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa mutanen da lamarin ya shafa karuwa ce da kuma kwastomanta.
Yadda lamarin ya auku
Wani Jami'in agaji na daban da ya nemi a boye sunansa saboda ba shi da hurumin magana da yan jarida yace:
""Mun ɗimauce da abinda idonmu ya gani, mutum biyu da aka zaro gawarwakinsu sun mutu ne suna tsaka da jima'i. Namijin ya haye karuwar lokacin da ginin ya rufta."
Wani jami'in kuma yace, "Ana amfani da wurin a matsayin wurin holewa (Club) kuma tabbas matar karuwa ce; Mace ta karshe da muka gano tana tare da Namiji, suna tsaka da jin daɗinsu lokacin da muka zaƙulo su."
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa zuwa yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton, ba'a gano iyalan mutanen biyu ba.
"Dole mu nemi abokanan kasuwancinta waɗanda suke mata masu zaman kansu domin samun bayani kan iyalan mamaciyar," inji majiyar.
A hukumance, LASEMA ta tabbatar da cewa ta gano gawarwakin mutum hudu, biyu maza, biyu mata.
A wani labarin kuma Wani Katon Bene Ya Ruguje, Ana Kokarin Ceto Wadanda Ya Danne a Legas
Wani katon bene ya sake rugujewa a titin Sonuga dake Palm Avenue a yankin Mushin dake Legas a Najeriya.
Kamar yadda shugaban hukumar bada agajin gaggawa, Olufemi Oke ya sanar, lamarin ya faru ne a ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng