Jami’an DSS Sun Hango Abin Tsoron da Suka Hango, Sun Yi Kira ga Malaman Jami’a
- Jami’an tsaro masu fararen kaya wanda aka fi sani da DSS, suna so a gaggauta janye yajin aiki a jami’o’i
- Darektan DSS na jihar Yobe yace rashin bude jami’o’in kasar nan zai imaida al’umma a halin La-hau-la
- Duba da hadarin rashin tsaro, Yunusa Abdulkadir yace za a iya komawa gidan jiya idan ASUU ta ki yin hakuri
Yobe - Vanguard tace DSS masu fararen kaya sun roki kungiyar ASUU ta malaman jami’a su hakura da yajin-aikin da suke yi a kusan duk fadin Najeriya.
A ranar Alhamis, 22 ga watan Satumba 2022, hukumar DSS ta fitar da jawabi tana rokon malaman jami’an kasar nan da su bude jami’o’i, a koma kan aiki.
Wani Darektan DSS da ke rike da jihar Yobe, Yunusa Abdulkadir ya gabatar da rokonsa ga ASUU a madadin gwamnati, da yake magana a Damaturu.
A karshen taron da Darektocin jihohin DSS suka yi a a garin Damaturu da ke jihar Yobe, Abdulkadir yace yajin-aikin jami’o’in gwamnatin yana da hadari.
ASUU na da gaskiya, amma ayi hakuri
“Duk da mun san ASUU tana korafi ne a kan abin da ya dace, amma suyi la’akari da kyau da Arewa maso gabas da ya dade a hannun ‘yan ta’adda.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Yunusa Abdulkadir
Darektan hukumar ya tunawa malaman jami’a cewa an yi fiye da shekaru 10 ana yaki da ‘yan Boko Haram, kuma rufe jami’o’i zai iya kara kawo hadari.
Watanni 7 ana zaman kashe wando
Tun watan Fubrairun shekarar nan, daliban jami’ar tarayya da ke garin Gashua da na jami’ar Yobe da ke garin Damatutu suka koma gidajen iyayensu a jihar.
Tsawon watanni bakwai kenan daliban jami’ar tarayya suna gida, an gaza sasantawa da gwamnati. DSS tace ya kamata ASUU ta yi duba ga illar zaman banza.
Asibitin mahaukata
Baya ga batun yajin-aiki, Abdulkadir yace akwai bukatar bude asibitin tabin kwakwalwa a Yobe saboda ayi maganin wadanda rikicin Boko Haram ya taba.
Jami’in na DSS yake cewa idan ba a magance matsalar da wadanda suka ga rikicin Boko Haram suke ciki ba, za su iya zama a zullumi wanda hakan barazana ce.
Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto cewa mataimakin gwamnan Yobe, Alhaji Idi Gubana ya halarci taron, ya yi alkawarin gwamnatinsa ta inganta tsaro.
'Yan Yahoo-Yahoo
Kun samu labari wasu kwararrun ‘Yan damfara watau Yahoo-Yahoo sun shafe kwanaki uku suna satar makudan kudi da mutane suka adana a bankuna.
‘Yan Sanda sun fara cafke wasu wadanda ake zargi da laifin satar wannan Naira Miliyan 523. An kuma kama wani mutumi da ya sulale da fam $120, 000.
Asali: Legit.ng