Yanzu-Yanzu: Wani Babban Na Hannun Daman Atiku Abubakar Ya Rasu
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi babban rashi na hadiminsa
- Babban sakataren Atiku, Barista Abdullahi Nyako, ya rasu a safiyar Alhamis, 22 ga watan Satumba
- Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda yace Nyako ya yi masa aiki cikin aminci ya mika ta'aziyarsa ga iyalan mamacin
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya rasa sakatarensa na musamman, Barista Abdullahi Nyako.
Daily Trust ta rahoto cewa Nyako ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis, 22 ga watan Satumba.
Atiku wanda shine dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP, ya tabbatar da rasuwar hadimin nasa inda ya mika ta’aziyya ga iyalansa.
Ya rubuta a shafinsa na Twitter:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Barista Abdullahi Nyako ya fi karfin hadimi a wajena, ya kasance dan uwa a gareni. Ya yi mun aiki da aminci da himma. Za a yi kewarsa sosai.
“A madadin iyalina, ina mai mika ta’aziyyata ga iyalan Abdullahi da addu’an Allah madaukakin sarki ya basu juriya da kuma karfafa su. Allah ya yafe masa kura-kuransa ya kuma bashi Aljannatil Firdaus. Ameen."
Kisan Ummita: An Gurfanar da ‘Dan Chana, Kotu ta Yanke Hukuncin Farko
A wani labarin, wata kotun Majistare da ke zama a kotu ta yi umurnin garkame ‘dan kasar China, Geng Quanrong, kan kisan masoyiyarsa yar Najeriya, Ummukulsum Sani Buhari.
Kotun ta yi umurnin tsare wanda ake zargin a gidan gyara hali na Kurmawa, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Umurnin kotun ya biyo bayan gurfanar da wanda ake zargin da yan sanda suka yi a gaban kotun kan tuhumar aikata kisan kai wanda yayi karo da sashi na 221 na Kundin Pinal Kod.
Asali: Legit.ng