Wani Ministan Ya Ci Alfarmar Buhari, Ya Samu Sarauta Mai Daraja a Masarautar Daura
Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya zabi karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva, zai ba shi sarauta
Timipre Sylva zai zama Sarkin Kudun Hausa saboda rawan da ya taka a gwamnatin Muhammadu Buhari
Tsohon Gwamnan ya yi wa Mai martaba Faruk Umar Faruk alkawarin cewa zai sauke wannan nauyi
Katsina - Mai martaba Sarkin Daura, Dr. Faruk Umar Faruk ya zabi karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva, domin ya ba shi sarauta a kasarsa.
Rahoton da Vanguard ta fitar ya bayyana cewa Sarkin Daura ya sanar da Timipre Sylva wannan a wata wasika da ya rubuta, ya kuma damka masa.
Sarkin ya shaidawa Ministan cewa zai ba shi sarautar “Sarkin Kudun Hausa”, a lokacin da ya kai ziyara ta musamman zuwa fadarsa da ke Daura.
Dr. Faruk Umar Faruk yake cewa tsohon gwamnan na Bayelsa ya samu wannan sarauta saboda cigaban da ya kawo, musamman a yankin Arewa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
This Day tace Basaraken ya fadawa Sylva daga yanzu yana wakiltar mutanen Arewacin Najeriya a yankinsa na Kudu maso kudancin kasar nan.
“Ina farin cikin sanar da kai cewa an ba ka sarautar ‘Sarkin Kudun Hausa’ domin godewa gudumuwar da ka ke ba ‘danmu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, Bayajida II.
Nasarorin da ka samu a ma’aikatar man fetur, abin-a-yaba ne, baya ga irin cigaban da kawowa Najeriya, musamman Daura. Za a sanar da kai ranar da za ayi maka nadin sarautar.”
- Sarkin Daura
Sarautar Hausa sai wane da wane
Rahoton yace Sarkin ya shaidawa Ministan cewa duk kasar Hausa, masarautarsa ce kadai take iya bada sarautar Hausa ga wanda aka ga ya dace.
A gefe huda, Sylva ya ji dadin wannan karramawa da masarautar mai tsohon tarihi tayi masa. Katsina Post ta fitar da wannan labari a rahotonta.
Ministan na man fetur ya nuna cewa daga yanzu zai dage wajen ganin ya sauke nauyin da aka damka masa na zama Sarkin Kudun kasar Hausa.
Bello Turji
Kun samu labari cewa kasurgumin ‘Dan bindiga, Bello Turji da wasu yaransa sun je yin sallah ne a sa’ilin da sojoji suka yi luguden wuta a sansaninsu.
Da alama Sojoji za su cigaba da addabar yankin da ‘yan bindigan suke. Hantar mutanen da ke wadannan kauyuka ta kada yayin da Turji ya shal.
Asali: Legit.ng