Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Alkalin Alkalan Najeriya

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Alkalin Alkalan Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta kaddamar da tantance mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, yau Laraba a zauren Majalisar dake Abuja.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Ibrahim Gobir, ya gabatar da kudirin haka misalin karfe 11:35 na safe, rahoton TheNation.

Mukaddashin CJN Ariwoola ya dira zauren majalisar kuma ya samu rakiyar dukkan Alkalan kotun koli, shugaban kotun daukaka kara, shugaban babbar kotun tarayya, shugaban kotun ma'aikatan tarayya da Sakataren majalisar shari'ar tarayya.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan lamuran majalisar dattawa, Sanata Babjide Omoworare, ya shigar da su majalisa.

Saurari karin bayani......

Ariwoola
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Alkalin Alkalan Najeriya Hoto: Presidency
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Asali: Legit.ng

Online view pixel