Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

  • Kotu ta umurci kungiyar malaman jami’a da ta dakatar da yajin aikinta da ke gudana a kasar nan
  • Alkalin kotun masana’antu ta kasa, Justis Polycarp Hamman, ya hana ASUU ci gaba da yajin aikin har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan shari’ar
  • Gwamnatin tarayya dai ta maka ASUU a kotu bayan sun gaza cimma matsala duk da ganawar da suke tayi akai-akai

Abuja - Labari da ke zuwa mana daga jaridar The Cable shine cewa kotun masana'antu ta Najeriya (NICN) ta umurci kungiyar malaman jami’a wato ASUU da ta janye yajin aikinta da ke gudana a fadin kasar.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki don ganin gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta ciki harda duba albashin malaman jami’a.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba Zamu Koma Aji Ba, Kungiyar ASUU Ta Daukaka Kara

Sandar kotu
Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki Hoto: Thisday
Asali: UGC

An yi tattaunawa da dama tsakanin malaman ASUU da gwamnatin tarayya amma duk sai a tashi ba tare da an cimma matsaya ba.

Saboda haka, sai gwamnatin tarayya ta garzaya kotu domin kalubalantar yajin aikin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnati ta hannun lauyanta, James Igwe, ta roki kotu da ta dakatar da ASUU daga daukar wasu matakai dangane da yajin aikin, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan shari’ar.

Da yake zartar da hukunci a Abuja a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba, Justis Polycarp Hamman ya amsa bukatar gwamnatin, jaridar Premium Times ta rahoto.

Legit.ng ta tuntubi wata lakcara wacce ta nemi a sakaya sunanta don jin ta bakinta kan wannan al'amari, inda ta nuna sam ba a yi masu adalci.

Ta bayyana cewa gwamnati bata damu da damuwar malamai ba alhalin sune iyayen ruhin kowani mutum don sune suke koyarda yadda mutum zai san ciwon kansa harma ya zama wani a rayuwa.

Kara karanta wannan

FG Zata Janye Rijistar Kungiyar ASUU, Ta Bayyana Dalilinta

Ta ce:

"Ta yaya za a nemi mu koma aji alhalin aljihunmu na bushe? Shin gwamnati ta damu da yadda muke rayuwa da iyalanmu tsawon wannan lokaci da muka yi babu albashi? Sam wannan ba shine adalci shugaba ba.
"Sai kuma yanzu a zo a nuna mana fin karfi ta hanyar tilasta mana komawa bakin aiki ba tare da bukatunmu sun biya ba. Wannan ya nuna karara gwamnati bata damu da damuwaru da na yaran da muke koyarwa ba.
"Zai fi dacewa a cimma matsaya guda kafin a koma aji ba wai a sa kotu ta tursasa mu komawa bakin aiki ba tare da wani kwakkwaran madafa ba."

Majalisar Wakilai Za Ta Gana da Buhari Bayan Cimma Matsaya da ASUU

A wani labarin, shugaban majalisar wakilai ta ce za ta gana shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i (ASUU), TheCable ta ruwaito.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan a jiya Talata 20 ga watan Satumba awanni kadan bayan ganawar sirri da shugabannin ASUU da karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah a majalisar dokokin kasar.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Ya ce da zarar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo, tabbas za su zauna dashi don tattauna sakamakon ganawar dashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng