Buhari Ya Kawo Gagarumin Cigaba A Bangaren Samar Da Wutar Lantarki A Najeriya, In Ji Femi Adesina

Buhari Ya Kawo Gagarumin Cigaba A Bangaren Samar Da Wutar Lantarki A Najeriya, In Ji Femi Adesina

  • Mr Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ya ce mai gidansa ya inganta lantarki Najeriya
  • Adesina ya ce sauran shugabannin Najeriya na baya sun gwada magance matsalar lantarki amma abin ya gaggare su
  • A cewar Adesina, sassan Najeriya da dama sun fara ganin cigaba a bangaren lantarki kuma za a cigaba da ganin canji saboda kwantiragin da Buhari ya yi da Siemens

FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya a daren ranar Talata ta ce wutar lantarki ta inganta a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari matuka idan aka kwatanta da yadda ta ke a shekarun baya.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV.

Femi Adesina
Buhari Ya Kawo Gagarumin Cigaba A Bangaren Samar Da Lantarki A Najeriya, In Ji Femi Adesina. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

Adesina ya ce kwantiragin da gwamnatin tarayya ta yi da kamfain Siemens ne yasa ake kawo transifoma da wasu kayan lantarki don magance matsalar dauke wuta a kasar.

Ya ce:

"Yan Najeriya ba za su ce ba su ga canji ba a bangare lantarki tun bayan hawan gwamnatin nan, yanzu na fada maka cewa an kawo wasu transifoma karkashin yarjejeniya da Siemens a baya-bayan nan. Hakan baya nufin cewa babu cigaba, akwai cigaba koma zai haifar da inganci a bangaren lantarkin kasar.
"Babu wanda zai yi musu cewa babu matsalar makamashi a Najeriya, musamman lantarki. Gwamnatoci a baya sun yi kokari sun gaza. Amma wannan gwamnatin ta samu fara inganta lantarkin kuma za a cigaba da ganin cigaba.
"A wasu sassan kasar, yan Najeriya sun fara ganin cigaba a bangaren lantarki kuma abin ba zai tsaya nan ba."

Ya cigaba da cewa:

"Mun yi yarjejeniya da siemens kuma ana samun cigaba, abin ya yi tafiyar hawainiya na wani lokaci amma cikin makonnin nan, mun ga ana ta kawo transifoma da kayan lantarki kasar. Ina tabbatar maka akwai cigaba.

Kara karanta wannan

Cefanar da NNPCL: 'Yan Najeriya ba Zasu Fuskanci Wuyar Man Fetur ba a Watan Disamba

"Shugaba Buhari ya mayar da hankali cewa kafin ya bar ofis a 2023, za a samu cigaba a bangaren lantarki kuma zai yi duk mai yiwuwa don cimma hakan."

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164